Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani a kan hanyoyin tafiyar da Gamin Gambizar Sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya. Da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.
Abinci masu kara dandano, zaki da karfin sha’awa ga ma’aurata:
1. Lansir: Wani ganye da ba kowa ya san shi ba amma yana da matukar alfanu wajen inganta lafiyar sha’awar ma’aurata domin yana dauke da sinadarin androsterone, maza na fitar da shi ta zufar jikinsu, in uwargida ta shake shi yana sa mata nishadin mijinta a zuci, wannan zai taimaka wajen motso mata da sha’awarta. Uwargida na iya yin kwadon lansir, da kuli ko da mai da yaji, ko ki sanya shi a saman shinkafa ko ma ku ci shi a haka yadda yake.
2. ’Ya’yan kabewa (kadawa, kabushi ko goji): Wannan wani abu ne da zubar da su muke yi duk lokacin da muka yi amfani da kabewa wajen yin miyar taushe cikin rashin sanin cewa sun fi ainihin tsokar kabewar amfani ga lafiyar jikinmu kuma musamman suna da matukar inganta ma’aikatar sha’awa. Cike suke da sinadarin Zinc, wanda da shi jiki ke amfani wajen sarrafa sinadarin sha’awa da kuma ruwan maniyyi, kuma shi ke inganta lafiyar Prostate gland, wani tsibirin sinadarai da ke kula da sarrafa ruwan maniyyi da kwayayen halittar da namiji. Sannan yana dauke da dukan bitamins masu inganta lafiyar sha’awa irin su C, D, E, K da kuma B mai rassa (B compled). Haka kuma yana dauke da sinadarin myosin da ke inganta lafiyar jijiyoyin ’yan matanci. Haka kuma yana dauke da sinadaran omega 3 wanda su ma suna inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa. ’Ya’yan kabushi suna da matukar amfani ga lafiyar jiki duka ba ga sha’awa kadai ba. In da ma’aurata za su iya, to su ci su haka yadda suke cikin kwansansu, sai sun fi ganin alfanunsu. Sun fi dadi in aka gasa su irin gashin da ake yi wa gyada, amma zafin na kone da yawan sinadarai masu alfanun da ke cikinsu. Uwargida na iya gyara su, ta cire kwanson, sai ta watsa su saman abinci in ya kusa dafuwa kamar dai yadda ake watsa tsanwar wake, karas ko kabeji. Sannan tana iya amfani da su wajen hadin salad ko ta nike su ta sanya cikin miyar taushe kamar yadda ake sa gyada, sai dai kada ta bari su sha wuta sosai.
3. Cakulet: Na dauke da sinadarin phenyl-ethylamine, wani sinadarin da ke haifar da nishadi da jin dadi cikin ma’aikatar hankali, irin jin dadin da masoya biyu kan ji farkon haduwarsu. In ma’aurata suka sha cakulet gab da gabatar da ibadar aure, za su samu karin so da karsashin ibadar auren dukkansu, wanda zai haifar da karin dandano da zakin ibadar auren gare su duka. Sai dai a kula, ba kowane cakulet ne za a saya ba, sai a nemi wanda kokon (cocoa) da yake ciki ya fi dukan kayan da aka hada shi da su yawa. Yawanci wadanda suka fi yawa a kasuwanni da kantuna zaki ne ya fi yawa a cikinsu, wasu kuma sai a cika su da gyada ko wafa. Hanya mafi sauki ta sayen cakulet mai kyau sai mutum ya ce a nuna masa wadanda suka fi tsada, domin dai an ce arha ba ta ado. Sannan sai a shashi a sannu musamman in mutum mai kiba ne domin yana dauke da sinadaran kara nauyin jiki.
4. Kwan Salwa: Na dauke da muhimman sinadaran gina jiki irin su Phosphorous, Proteins, da bitamin B, D da E, don haka yana matukar inganta lafiyar ma’aikatar sha’awa, sinadaran cikinsa na kula da kuma zaburar da masarrafin maniyyi-Prostate gland. Yana kara karfin motsuwar sha’awa da kuma karin kuzarin sha’awa. Ana sarrafa shi don ci kamar yadda ake sarrafa kwan kaza, amma ya fi alfanu in aka sha shi yadda yake domin ba ya da wani karni ko wari mai sa tashin zuciya.
5. Waken soya: Da duk wani abin da aka hada da shi, irin su awara, madarar waken soya, da sauransu na inganta ma’aikatar sha’awar ’ya mace musamman wajen tabbatar da isasshiyar lema a ’yan matancinta domin yana dauke da sinadarin Phytoestrogen wanda ke yanayi da sinadarin ’yan matanci estrogen. Ga uwargida da ke fama da matsalar isasshiyar lema, sai ta rika shan kofi daya na madarar waken soya sau daya a rana, amma ban da mai matsalar cutar daji domin akwai yiwuwar sinadaran cikin waken soyar su sake dawo mata da ciwon. Maigida ya guji cin waken soya ko duk wani abu da aka hada da shi, sai dai in yana son rage sha’awarsa ne, domin wannan sinadari phytoestrogen yana dakushe karfi da yalwar sinadarin mazantaka da sha’awa, watau testosteron.
Sai mako na gaba sauran bayani na zuwa, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.