Warin gashin kai yana daya daga cikin abubuwan da suke ta da wa mata da dama hankali. Sai a ga mace ta yi ado ta fito tsaaf, amma ana jin wari.
Ba wani abu ba ne illa warin da ke tashi daga gashinta. Saboda matsalar fatar kai na janyo warin gashin kai.
- Mutum 9 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
- Gobara ta yi kisa a sansanin ’yan gudun hijira a Maiduguri
Yawan sa man gashi na dada warin gashi, musamman idan man ya yi yawa a gashin kuma ya hadu da ruwa sai gashi ya fara wari.
Yawan barin gashi ya yi dauda sosai ma na janyo warin gashi.
- Idan za a sayi man wanke gashi (shampoo) a sayi wanda ke dauke da sinadarin sulphur ko zinc ko mai dauke da anti-bacterial.
- Man wanke gashin kai mai dauke da sinadarin silicyl na magance wadannan matsaloli.
- Za a iya amfani da lemun tsami domin magance warin gashin kai. Bayan an wanke gashin da man wanke gashi, sai a matse lemun tsami a hada da ruwa a yi wa gashin wankin karshe.
- Ruwan tumatir na magance warin gashin kai. Kafin a wanke gashi da man wanke gashi, a matse ruwan tumatir sannan a shafa a fatar kai. A jira na tsawon minti 10 kafin a wanke da man wanke gashi (shampoo).
- Ana iya hada ruwan ganyen dogon yaro da man wanke gashi, a juya shi sosai kafin a fara amfani da shi, yin hakan na rage warin gashin kai.
- Za a iya samun man gashin ka da ke dauke da man labender domin samun kamshin gashi a koyaushe.