A ’yan makonnin nan an samu karuwar yawan barkewar wannan ciwo a wasu sassa na arewacin kasar nan. Shi wannan ciwo da ma can yakan kama mutane jefi-jefi kuma ya ma fi saurin yaduwa fiye da zazzabin Ebola, saboda kuda ma, wannan da muke zama da shi, shi kadai zai iya yada shi ko’ina.
Ciwon kwalara ko kuma ciwon amai da zawo, kamar yadda aka fi sani, ciwo ne da idan aka daure aka bi shawarwarin ma’aikatan lafiya kuma hukumomi suka dauki nasu matakan yadda ya kamata, to zai iya zamowa daya daga cutukan da aka kawar a bayan kasa. kasashen da suka ci gaba su ma a da sun yi fama da annobar wannan ciwon, amma yanzu sun shawo kansa. A yanzu an fi ganin shi a irin kasashenmu, inda duk shekara sai ciwon ya halaka dubunnan mutane, akasarinsu kananan yara. Ba da wata allurar riga-kafi ake yakar wannan ciwo ba, da tsabta ce kawai sauran kasashen duniya suka ga bayansa. kwayoyin cutar bacteria da ake kira bibrio cholerae, su ke kawo shi.
Yaya ake kamuwa, yaya kuma ake gane alamun ciwon?
kwayoyin cutar suna rayuwa ne a gurbataccen ruwa. Idan aka sha, sai su shiga ciki su je su makale a jikin ’ya’yan hanji. Nan da nan cikin ’yan awoyi sai zawo, amma ba ciwon ciki. Wasu sukan yi amai. Kafin gari ya waye mutum ya fada, ba kuzari, ruwan jikinsa ya kare. Idan ba a dauki matakin gaggawa ba, rai zai iya yin halinsa; Idan babba ne akan dauki lokaci kafin ya galabaita. Yara ’yan shekara 1-5 da haihuwa da tsofaffi su aka fi rasawa. Manya sukan iya kamuwa da kwayar cutar ba tare da sun yi amai ko zawo ba, sai dai su yada.
Ciwon na yaduwa ne kamar wutar daji ta hanyoyi uku: kuda yakan dauko kwayoyin cutar a amai ko zawon da mai cutar ya yi, ya taba abinci ko ruwa. Hanya ta biyu kuma ita ce mutum ya taba amai ko zawon mai cutar ya ci abinci bai wanke hannu ba. Hanya ta uku kuma idan mai dauke da kwayar cutar ya yi ba haya ko zawo kusa da ruwan da jama’a ke amfani da su walau rijiya ko kogi da sauransu.
Hanyoyin Kariya Daga Wannan Ciwo?
1. A tabbatar an tace sa’annan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha. Ruwan famfo na hukuma yana da sinadarin chlorine da kan iya kashe kwayoyin cutar. Ba shi da dandano, amma a wasu lokuta akan ji kanshinsa idan an shaki ruwan a hanci. Shi ma wanda ba a sa wa wannan sinadari ba, kamar ruwan da ake da shakku a kai, ta kamshi da dandanonsa akan gane ko da a ido garai-garai yake.
2. A guji irin ruwan shan nan da ake sawa a leda a yanzu a ce wai ‘pure water’ ne, domin yawanci a yanzu samun nagari a cikinsu, sai an tona. A gida kawai wasu ke zama su kulla. Yawancinsu idan mutum ya dauka ya haska da fitila a daki mai duhu zai ga wasu giza-gizai, wanda idan ba a lura ba, za a iya sha kuma su kawo matsala.
3. Ruwan rijiyar burtsatse irin mai zurfin nan sosai, in dai ba ta gurbata da wani abu ba, yakan ma fi wasu ruwan ledar kyau da lafiya.
4. Da zarar an ga alamun ciwon, a samo ruwan gishiri da sukari na sachet wato ORS a hada a fara ba maras lafiya kafin a garzaya asibiti mafi kusa. Idan ba a samu ORS ba, a samu gishiri rabin karamin cokali da sukari cikin karamin cokali goma a hada a ruwa mai tsafta kwatankwacin babban kofi, a bayar a hankali har a kai asibiti.
5. Dole a tafi asibiti domin a duba maras lafiya sosai a ba shi magani ko karin ruwa saboda maras lafiyan zai iya amai ya dawo da ruwan gishirin da aka ba shi.
6. A asibiti akwai kwayoyin magunguna na riga-kafi da ake ba wadanda ke jinyar masu wannan ciwon.
7. Hukumomin gidan ruwa su tabbata an saka sinadarin chlorine yadda ya kamata kafin a sako ruwa.
8. A guji shan kankara da ba a tabbatar daga ruwan da aka hada ta ba. Idan ya zama dole, a ribanya ledar jikin kankarar kafin a sa a ruwa mai tsabta don ya yi sanyi.
9. A tabbata an wanke hannaye da sabulu bayan an yi bayan gida da kuma kafin cin abinci. Yawan wanke hannu da sabulu yana hana kamuwa da wannan ciwo kwarai da gaske.
10. Masu sayar da abinci su guji taba abin sayarwar da hannu, sai da babban mazubi ko marar zuba abinci.
11. A kiyaye tsabtar muhalli da ta bayan gida don kada kuda da kyankyaso su samu wurin zama.
12. A rufe duk wani abinci da abin sha don kada kuda ko kyankyaso ya hau.
13. Kada a ci kayan lambu irin su latas da karas da ba dafa su ake yi ba, har sai an wanke su a ruwa mai gishiri an kuma dauraye. A yi ta wankewa sai an daina ganin kasa-kasa.
14. A guji yin bahaya a kusa da magudanar ruwa ko rijiya ko kogi.
15. Kada a gina rijiya dab da matattarar bayan gida wato sokawe, a ba da tazarar a kalla kafa 50.
16. Gina gidajen ba-haya na zamani masu inganci a wuraren zaman jama’a kamar kasuwanni zai rage yawan ba haya barkatai, a kusa da magudanun ruwa.
LAFIYAR MATA DA YARA
Amai
Amsoshin Tambayoyi
Ina da yaro dan shekara daya da wata bakwai wanda na ga kamar bugun zuciyarsa da sauri-sauri ba kamar na sauran yara ba. Banda wannan, kamar dai lafiyarsa kalau. Na kai shi asibiti likita ya ce ba komai, amma ko taba shi bai yi ba. To ko na koma da shi?
Daga Samira, Katsina
Amsa: A’a, in dai yana wasansa da guje-gujensa ba tare da yin haki ko saurin gajiya ba, ba komai. Duk da haka dai tunda har an samu an kai shi asibiti, da kamata ya yi a ce likitan ya duba shi ya auna yawan bugun zuciyar a minti guda, ya kuma saurari bugun zuciyar da abin saurare. Ke za ki iya aunawa da kanki, amma ki bari sai yana barci ki sa hannunki kan kirjinsa, inda kike ganin bugun zuciyar, ki auna sau nawa take bugawa a minti guda. Kin ga ke nan sai kin sa agogo mai hannu a gaba. Da yake yaro ne karami za ta iya bugawa har kusan sau 120 ma idan yana barci a minti guda, ko 160 idan yana guje-guje. Don haka sai kin ga ya haura wadannan za ki maida shi, idan ba su wuce haka ba, ki kwantar da hankalinki.
Ni nakan samu doguwar nakuda idan na zo haihuwa. Shi ne nake tambaya tsarin lafiyar kasashen waje wajen yin allurar rage zafin nakuda. Shin akwai abin da ake ba mace ko su ma ba sa bayarwa?
Daga Maman Abu, Kano
Amsa: E to, a kasar waje akan kwatanta kamanta ba wa kowa hakkinsa, har maras lafiya. Ya kuma danganta da matar da kuma asibitin. Idan mace ta san da allurar kuma ta tambaya a asibitin kudi, kin ga ke nan a cikin kudin da za ta biya ake sa lissafi. Idan kuma asibitin hukuma ne ba dole ba ne a ba ki allurar, sai an ga kin nace. Ala-aiyi-halin dai duk abin da ya wuce awa goma sha ana nakuda ba a haihu ba, in dai a asibitin da suka san me suke yi ne, dole su dauki matakin taimaka miki ki haife da sauri, kamar sa ruwan yaji, ko janyo jaririn da kayan aiki idan an ga kamar shi ne ya makale, ko kuma a yi miki tiyata. Amma a ce ki kwana biyu kina nakuda, kamar yadda kika ce, in dai a asibiti ne kika yi wadannan kwana biyun, sai dai a ce ki canza asibiti.
Wadanne irin illoli ne kan faru ga mata masu yunkurin zubar da juna biyu ta hanyar shan kwayoyi?
Daga El-Musty, Kaduna
Amsa: Yawanci matsalar ta fi faruwa a kan jariran. Wasu sukan samu nakasa tun suna ciki sakamakon yunkurin halaka su da magani da aka yi; wasu ma su mutu gaba daya a cikin, a yi barinsu; wasu kuma wadanda suka fi watanni uku idan suka mutu a cikin mahaifar sukan yi zamansu, sai an ji shiru kafin a farga, wanda wannan shi ne zai iya kawowa matar matsala, wato da ya mutu a cikinta ya dade bai fita ba. Akwai matsaloli iri-iri da aka alakanta da hakan, kamar tsinkewar jini, ba na mahaifa ma kawai ba, har da sauran sassan jiki.