✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyin kariya daga ciwon kazwa

Mene ne maganin kazwa?Daga Mansur, KeffiAmsa: Kafin a fada maka maganin kazwa, sai an tabbatar kazwar ce, domin akwai kuraje iri-iri da kan fito a…

Kwaron da ke kawo kazwaMene ne maganin kazwa?
Daga Mansur, Keffi
Amsa: Kafin a fada maka maganin kazwa, sai an tabbatar kazwar ce, domin akwai kuraje iri-iri da kan fito a jiki masu kama da kazwa, kamar makero ko tautau ko kurajen borin jini, ko kuraje sakamakon shan wasu magunguna masu fasa fata, ko ma kurajen ciwon sanyi na tunjere. Bayan an yi maganinta kuma akwai hanyoyin kiyaye dawowar ciwon, wadanda idan ba a bi su ba, ciwon zai iya dawowa.
Ita kazwa, wani irin ciwon fata ne mai wuyar sha’ani, mai wuyar magancewa. Ba kwayoyin cuta ba ne ke kawo kazwa ba, kwari ne masu kama da kwarkwata ko kudin cizo, sai dai saboda kankantarsu, su ba a iya ganinsu da kwayar ido. Matsalar ita ce idan kwarin da ke kawo kazwa suka shiga gidan mutum, sai an yi da gaske kafin su fita, don haka za a ga ba mutum daya kawai sukan kama ba, kusan duk mutanen gidan. Sun fi nunawa a yara, saboda rashin karfin garkuwar jiki. Manya masu kwarin garkuwar jiki ba su cika nuna kuraje da kaikayi ba idan kwarin suka shiga karkashin fatarsu. Don haka su ma manya za su iya zama sila wajen yada wa yaransu wadannan kwari. Wato a wasu lokuta ba yara ne ke kwaso ciwon ba, manya ne ke yada wa yara, amma da yake bai cika saurin nuna alamu a manya ba, sai a dauka yara ne suka kwaso.
kazwa kan iya kama kowane jinsi, fari ko baki, mai kudi da maras shi duka, sai dai ta fi kama maras shi, saboda mai hannu da shuni kusan gidansa da fadi kuma ba cinkoson wurin kwanciya. Amma kowa ya san akwai kuma gidajen masu hannu da shunin da na wani talaka ya fi shi tsabta. Su kurajen kazwa sukan iya fitowa a ko’ina: a hannu, ko a kafa, ko gadon baya da matse-matsin cinyoyi da sauransu, amma sun fi fitowa a tsakankanin yatsun hannu, kuma suna da kaikayi sosai, wanda kan hana mutum sakat, kuma tabonsu yakan dade bai bace ba, kamar na fitsarin gwauro.
Bayan an tabbatar su ne, akan ba da magani. Kuma kamar yadda aka zayyana a sama, akwai sharudda da akan gindaya yayin amfani da maganin, domin kada su dawo. Duk zannuwan gadon mai wannan matsala da soson wanka da tawul, sai an canza su an sayi sabbi. Kayan sawa kuma dole sai an wanke an shanya a rana an kuma goge su da dutsen guga mai zafi sosai gaba-daya yayin da ake amfani da maganin, domin kwaro daya idan ya rage, zai iya sakin kwayaye. Sunan maganin shafawar permethrin. Yana da wuyar samu, sai an je babban kyamis. Wani magani ma benzyl benzoate yana iya kashe kwarin, shi ana samunsa sosai, amma bai kai wancan na farko ba. Shi ya sa da za a so duk masu matsalar su je asibiti a tabbatar a rubuta musu shi mai karfin, domin ana iya samu a asibitoci. Ana game jiki gaba daya da maganin ne banda kai, don kada maganin ya shiga ido da baki (amma ana hadawa da wuya da bayan kunne). Bayan kamar awa takwas a yi wanka a wanke maganin, bayan kwana biyu a sake shafawa idan an ga alamun ba su tafi ba, amma kar ya wuce sati daya.

Hanyoyin Kariya:
1.    Dole a rika yi wa dukkan yaran gida wanka a kalla sau daya a rana, don yawan tsabtar jiki takan iya kiyaye kamuwa, saboda ko da yaran gidan ba su da shi, za su iya kwaso kwayayen a wurin wasu yaran a makaranta ko wurin wasa, amma yawan wanka kan iya kiyaye su.
2.    Don haka kuma ke nan dole a kiyaye wuraren da yara ke zuwa wasa.
3.    Idan akwai almajiri mai yin hidima a gidan mutum, dole a kula da tsabtarsa, kamar yadda za a kula da ta yaran gida ko kuma a kalla rika sa shi wanka kullum da wanki akai-akai.
4.    Dole a raba wurin kwanciyar yara, a ba kowa shimfidarsa daban, don a haka duk wanda ya samo ciwon zai yi wuya ya raba wa sauran. Idan wurin kwanciya daya ne, ba makawa, sai ya yada kwarin.
5.    Tsabtar cikin gida tana da matukar muhimmanci wajen kiyaye zaman kwarin a cikin gidan. Duk lunguna da wasu shirgi da kananan ramuka sukan iya boye wadannan kwari, idan aka yi sake suka shigo gida, sukan iya rayuwa ko ba a jikin mutum ba, na kusan kwana biyu zuwa uku, amma kafin su mutu sukan saki kwayaye. A haka su yi ta yaduwa.
6.    Idan mutum daya ya samu kazwa a cikin gida, ana so kowa a gidan ya je ya karbi maganin da aka ba mai ciwon, shi ma ya shafa, ko yana da alamu ko ba shi da alamu.
7.    Dole mai ciwon kuma, wanda ya nuna alamu ya guji mutane na tsawon lokacin da aka ce ya shafa maganin don kada ya yada kwarin, wato tsawon kwana uku ko sati guda.
8.    A kwanakin shafa maganin, sai mai ciwon ya rika wanke kayan sawarsa a ruwan zafi, ya shanya su a rana; a kuma goge da dutsen guga mai zafi don kashe duk kwarin.
9.    Zannuwan shimfida da kayan wankan mai ciwon, duk sai an canza su bayan an warke, idan kuma ba hali akan dauke su a sa a katuwar bakar leda a daure a adana na tsawon sati kafin a fito da su a wanke a goge, don idan ba hakan aka yi ba, ba tabbas cewa kwarin sun mutu, tunda ba ganinsu ake da kwayar ido ba.
10.     Dole hukumomin gidan yari da na gajiyayyu su san wannan matsala su rika wayar wa fursunoni kai a kan ciwon, su kula da tsabtarsu, su ware musu matsalar a daki na musamman su kuma samar musu da magunguna, har sai sun warke, domin ana samun matsalar sosai a gidan kaso, musamman wadanda suke da cinkoso. Dole su yi wannan ko don su ma su kare kansu da iyalansu. Wasunsu da dama suna iya kwasar ciwon su kai gida. Da yawan ’yan fursuna, a irin wadannan gidaje, sabulan wanka ma sai mutanen gari ne ke kai musu sadaka jefi-jefi.

LAFIYAR MATA DA YARA

Amsoshin Tambayoyi

Likita mene ne ciwon ela? Kuma ko shin yana da maganin asibiti ne ko kuwa? Ina da yaro dan wata uku mai ciwon, kuma duk sauran yarana sai da suka yi ciwon.
Maman Khalid
Amsa: Abin da na binciko a kan wannan ciwon na ela, wadda kalma ce ta Yarabanci, shi ne ciwon na nufin ciwon fata, wanda kwayar cutar fungus kan kawo wa jarirai. A likitance akwai cutukan fata da dama, wadanda kwayar cutar fungus kan kawo, don haka mu a likitance cutukan fata kusan sai mun gani muke tantancewa, duk da cewa mun san yawa-yawan cutukan fata wannan kwayar cuta ce ke sawa. Amma muna gani ne don mu tantance ko hakan ne ko ba haka ba, don akwai kuma wasu matsalolin jiki da kan fara nuna alamu a fata, musamman a jarirai.
Idan kuma a duwawu ne wurin da ake sa famfas ko napkin da sauransu, ana yawan samun kwailewar fata saboda danshin fitsari, wanda kan iya kawo zaman kwayar cutar a wurin, tunda ta fi son danshi. Idan wannan ne, za ki iya fara sayen man shafawa na sudocream mai kashe kwayar fungus, har ila yau kuma ya kare fatar jaririn daga illar gubar fitsari. Shi wannan maganin shafawa na yara ne kuma shi ba sai da sa hannun ma’aikacin lafiya ake samunsa ba, a rika shafawa kafin a daura famfas. Idan sun ki mutuwa to ke ma kin san sai likita ya gani.
Idan aka haifi jariri ba a yi masa aski ba har tsawon wata guda hakan akwai matsala?
Daga Auwalu
Amsa: A’a, ba wata matsala a likitance.
Na ji ka ce yawan shan kwayar aspirin ga mai ciwon mara na al’ada yana iya kawo matsala. To ni feldene da panadol edtra na fi sha. Ko su ma akwai matsala?
Daga Maryam,
Amsa: E, feldene da cataflam da brufen duk dangogin aspirin ne, kuma suna iya kawo gymbon ciki dukkansu idan aka damu da sha akai-akai. Muna yawan ganin masu samun olsa sakamakon shan wadannan magunguna ba ka’ida na tsawon lokaci, daga baya yawancinsu olsar ce ke ajalinsu idan ta huje suka fara aman jini. Panadol ne dai kawai ba a danganta da irin wannan matsala ba, shi ma ana dangata shi da ciwon hanta idan aka maida shi kamar abinci. Akwai wasu magungunan kashe ciwon marar masu karfi wadanda sai an rubuta miki za ki iya sayensu. Don haka idan panadol bai yi aiki ba, watakila sai kin je an rubuta masu karfi irin wadannan din.