A ranar Asabar ne za a yi zaben Shugabana Kasa da na ‘yan Majalisar Tarayya, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta tsara.
Sai dai zabe na iya zuwa da wasu al’amura; wasu masu dadi wasu kuma akasin haka.
- Nawa ’yan siyasa ke batarwa wajen dinka suturar yakin neman zabe?
- Kowa ya zabi dan takarar da yake so —Sheikh Dahiru Bauchi
Don haka, yana da kyau wanda zai je rumfar zabe domin kada kuri’a, ya tabbatar ya bi matakan da zai kare kansa daga fada wa wani rikici ko hatsari.
Ga wasu daga cikin hanyoyin da mai zabe ya kamata ya kare kansa a lokacin zabe:
1. A guji musu a kan siyasa a bainar jama’a: Yana da kyau wanda ya je yin zabe, ya yi abin da ya kai shi, wato ya kada kuri’a ya bar wajen. Yin musu ko takaddama a kan siyasa na iya harzuka wani ko wasu a fara rigima, don haka ya kamata mai zabe ya guji aikata wannan.
2. Ka da a soki wani dan siyasa a wajen zabe: Yana da kyau wanda ya je kada kuri’a ya guji ko haramta wa kansa sukar wani dan siyasa, domin wasu magoya bayansa na iya daukar mataki ko martanin da ka iya haifar da tashin-tashina.
3. Ka da a saka kaya ko alamar wata jam’iyya: A matsayinka na mai zabe, ka guji saka wasu nau’in kaya ko wata shiga da ke nuna wani bangare na siyasa, domin bata-gari na iya amfani da wannan dama wajen cutar da kai.
4. A rufe mota da makulli yayin da ake tuki: Yana da kyau idan da mota mutum yake yawo ranar zabe, ya tabbatar da cewar ya rufe ta saboda gudun ta baci, ko kuma wasu da ka iya kokarin bude masa mota yayin da wani abu ya taso.
5. A guji yawon dare: Yana da kyau ga wanda zai yi zabe ya guje wa yawace-yawacen dare. A irin wannan lokaci jami’an tsaro na bayar da umarnin lokutan da mutane za su yi zirga-zirga, don haka yana da kyau a bi wannan doka don zama lafiya.
6. A guji wallafa abin da zai tada tarzoma a kafafen sada zumunta: Wannan ya shafi mutanen da ke amfani da kafafen sada zumunta. Yana da kyau a guji wallafa labarai na karya, hoto, bidiyo ko nau’in wani abu da zai iya tunzura wasu a fara rikici.
7. A guji zama cikin mutanen da ba a sani ba: Yana da kyau ga mai zabe da zarar ya kada kuri’arsa ya har wajen zaben. Idan ma mutum ya tsaya a wajen yana da kyau ya dan yi nesa da wurin kada kuri’a ko kuma a guji zama cikin gungun mutanen da ba san su ba.
8. A dinga bibiyar labarai: Yana da kyau a lokacin zabe mutane su rika bibiyar kafafen watsa labarai don sanin irin wainar da aje toyawa. Wato idan akwai labarin wani waje da aka samu tashin hankali mutum zai sani kuma zai kaucewa fada wa rugumtsimi.
9. A tanadi lambobin kira na kar-ta-kwana: Yana da kyau ga duk wanda zai je wajen zabe ya ayyana wata lamba ko lambobi da zai iya kira kai tsaye daga wayarsa don neman dauki idan wani abu wanda ba a fata ya faru za a kai masa dauki cikin gaggawa.
Wadannan kadan ne daga matakan kariya da duk wani mai zuwa wurin zabe ya kamata ya bi su don zama lafiya.