Kasar Jamus ta tabbatar da daukar kocin Bayern Munich, Hansi Flick a matsayin wanda zai maye gurbin mai horas da ’yan wasanta, Joachim Low, da zarar an kammala gasar cin kofin Euro 2020.
Bayan ajiye mukaminsa, Flick zai dauki gabarar jagorantar tawagar ’yan wasan kasar Jamus.
- Kwalara ta kashe 20 wasu 322 sun harbu a Bauchi
- EURO 2020: Babu dan wasan Real Madrid a tawagar Spain
Jamus ta fitar da sanarwar daukar sa ne a ranar Talata, inda ya rattaba hannu na tsawon shekaru uku, zuwa karshen kakar wasanni ta 2024.
Flick, zai ke daukar Fam miliyan 6.5 a duk shekara, kasa da abin da yake dauka a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich.
Tun kafin kakar wasanni ta bana ta kare, bayan sanar da cewar zai bar Bayern Munich aka shiga yada jita-jitar zai karbi aikin horas da tawagar kasar Jamus.
Shugaban Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona Joan Laporta, ya jima yana zawarcin Flick domin ya karbi kocin Barcelona.