Kotu ta yanke hukuncin daurin shekera biyu a gidan yari ga Fatima Jibril, budurwar Abdulmalik Tanko, wanda ya kashe dalibarsa mai shekara biyar, Hanifa Abubakar.
Kotun ta yanke wa Fatima hukuncin ne a ranar Alhamis, tare da Abdulmalik da abokinsa Hashimu Isyaku hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin sacewa da kashe Hanifa.
- Hanifa: Kotu ta yanke wa Abdulmalik Tanko hukuncin kisa ta hanyar rataya
- ’Yan bindiga sun halaka sama da mutum 20 a kauyukan Zamfara
“Wadda ake zargi ta uku (Fatima Jibril) kuma a matsayinta na uwa an yanke mata hukuncin daurin shekara daya kan laifin yunkurin garkuwa da wani shekara daya kuma saboda hadin baki,” inji alkalin kotun.
Mai Shari’a Usman Na’abba, ya kuma yanke wa Abdulmalik karin daurin shekara biyar a gidan yari, shi kuma Hamisu karin daurin shekara uku a kurkuku.