Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba 6 da ke zamanta a Sakatariyar Audu Bako, karkashin jagorancin mai shari’a Usman Na’abba, ta yanke wa malamin nan da ake zarginsa da kisan dalibarsa, Hanifa Abubakar, Abdulmalik Tanko, hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samunsa da laifin yin garkuwa da ita da kuma kisanta.
Haka kuma kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara biyar saboda samunsa da laifin hada baki da kuma boye ta.
- NAJERIYA A YAU: Matsalar Tsaro Za Ta Iya Kawo Wa Zaben 2023 Cikas
- Barcelona ta sayi Jules Koundé daga Sevilla
Shi ma Hashim Isyaku, wanda ake zargi da laifin hada baki da taimaka wa Abdulmalik Tanko wajen binne gawar Hanifa, kotun ta yanke masa hukuncin kisa da kuma hukuncin daurin shekara biyar a gidan gyaran hali.
Haka kuma kotun ta yanke wa budurwar Abdulmalik, Fatima Jibril Musa, hukuncin daurin shekara biyu a gidan gyaran hali saboda samunta da laifin hada baki da kuma yunkurin yin garkuwa.
Yayin yanke hukuncin, alkalin kotun mai sharia Usman Na’abba, ya ce kotun ta yanke wannan hukunci ne bisa gamsuwa da shaidu da hujjoji da masu gabatar da kara suka gabatar a gabanta.
Tun da farko mai gabatar da kara Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya nemi kotun da ta yanke wa wadanda ake tuhuma hukunci mai tsanani daidai da laifin da suka aikata.
Sai dai lauyoyin wadanda ake kara karkashin jagorancin, Barista Asiya Imam, sun nemi kotun ta saukaka wa wadanda ake tuhuma kasancewar suna da iyali wadanda nauyinsu ya rataya akansu.
Haka kuma a cewar lauyoyin wacce ake tuhuma ta uku, Fatima Jibril Musa uwa ce da ke da karamin goyo.
Idan za a iya tunawa tun a ranar 24 ga Janairu 2022, gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da Abdulmalik Tanko mai shekara 34 da Hashim Isyaku mai shekara 37 da kuma Fatima Jibril, dukkaninsu mazauna unguwar Tudun Murtala a gaban kotun bisa zarginsu da aikata laifuka guda hudu da suka hada da hada baki da na garkuwa da na boyewa da kuma na kisa, laifukan da suka saba da sashe na 97 da na 274 da na 277 da na 221 na kudin shari’a na final Kod.
Takardar karar ta bayyana cewa a ranar 4 ga watan Disamba 2021, Abdulmalik Tanko wanda malamin makarantar Noble Kids School da Hanifa Abubakar ‘yar kimanin shekara biyar a duniya, ya sace ta tare da boye ta a daidai lokacin da take dawowa daga makarantar Islamiyya, inda ya ajiye ta a gidansa tsawon kwana shida.
“Daga bisani ya nemi kudin fansa Naira miliyan shida daga mahaifanta, inda ya fara karbar N100,000 a matsayin somin tabi.
Takardar karar ta ci gaba da cewa “Bayan wasu kwanaki Abdulmalik ya kashe Hanifa ta hanyar ba ta shinkafar bera, inda kuma ya hada kai da Hashim Isyaku ya binne ta a wani bangare na wata makarantarsa Northwest Preparatory Scholol da ke unguwar Tudun Murtala bayan ya gutsttsura gawarta ya dure a cikin buhu.”
Sai dai wadanda ake zargi sun musanta aikata laifin kisan, inda suka amince da laifin hada baki da yin garkuwa da kuma boye Hanifa.