✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hana sayen kuri’u ba aikinmu ba ne —INEC

Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) ta ce ba aikinta ba ne hana sayen kuri'u a lokacin zabe.

Hukumar Zabe ta Najeriya (INEC) ta ce ba aikinta ba ne hana sayen kuri’u a lokacin zabe.

Kwamishinan INEC na Jihar Osun, Farfesa Abdulganiy Raji, ne ya bayyana haka a lokacin da aka tambaye shi game da matsalar sayen  kuri’u gabanin zaben gwamnan jihar da ke tafe ranar Asabar.

Ya ce, “Saye da sayar da kuri’u babban laifi ne amma INEC ba hukumar tsaro ba ce mai ikon tsare masu laifi.

“Iya abin da za mu iya shi ne mu sanar da hukumomin tsaro idan muka ga ana yi (sayen kuri’u); daga nan sai su tsare wadanda ake zargi su gurfanar da shi a gaban kotu.

“Nakan yi mamaki masu maganar cinikin kuri’u da ke tunanin INEC ce za ta hana, alhali hanawan ba shi da wani lakada da aikin hukumar na gudanar da zabe.

“Su masu cinikin kuri’un ya kamata a yi wa magana,” ko da yake ya ce hukumar za ta yi aiki da muhimman masu ruwa da tsaki wajen shawo kan matsalar.

Matsalar sayen kuri’u dai na ci wa harkar zabe a Najeriya tuwo a kwarya.

Ko a zaben Gwamnan Jihar Ekiti da aka gudanar a makon ci an yi fama da ita sosai.

A ranar Laraba, Shugaban Kwamitin Zaman Lafiya, Rabaran Atta Barkindo, ya bayyana damuwarsa kan matsalar sayen kuri’u a lokacin zabe a Najeriya.

Ya bayyana damuwa cewa a yayin da zaben gwamnan Osun ya karato, akwai mutanen da ke jira su sayar da kuri’unsu, saboda tsabar talauci a Najeriya.

Amma Farfesa Raji ya ce, “In dai maganar sayen kuri’u ne, to ina tabbatar maka cewa INEC ba za ta iya hanawa ba.

“Za dai mu iya kokari wajen sanyaya wa mutane gwiwa su daina ta hanyar wayar da kan masu zabe kamar yadda muka saba yi”.