Mayakan Falasdinawa sun harba makaman roka sama da 200 a kan Isra’ila daga Zirin Gaza.
Rundunar Tsaron Isra’ila (IDF) ta sanar a safiyar ranar Talata cewa kungiyoyi a Gaza sun yi ta harba rokoki “babu kakkautawa” na tsawon awa 10.
- An hana zuwa Filin Idi a Abuja —Minista
- Karamar Sallah: ‘Ba za a ga wata ranar Talata ba’
- An yi fashi a kusa da Fadar Shugaban Kasa
IDF ta ce wani roka ya fadi a kan wani gini a garin Ashkelon a kudancin Isra’ila. Wani rahoto ya ce gine-gine biyu ne, ma’aiaktan jinya kuma sun ce an jikkata mutum shida a garin.
Rundunar Al-Qassam, reshen soja na kungiyar Hamas, ta ce luguden wutar da aka yi wa Ashkelon ramuwar gayya ce ga sojojin Isra’ila da suka far wa wani gini a Yammacin Zirin Gaza.
Isra’ila ta harba rokoki 130 zuwa Gaza
Wani kakakin IDF ya ce Isra’ila ta kakkabo kashi biyu bisa ukun makaman rokan da haka harbo mata tun kafin su baro Zirin Gaza.
Ya ce yawan rokokin da aka kakkabo na iya sanadin mace-mace a Gaza.
Isra’ila, a cewarsa ta mayar da martani da harba rokoki kusan 130 a kan wasu wurare da ke Zirin Gaza, inda ta kashe 15 daga cikin ’yan kungiyoyin Hamas da Jihadin Islama.
A cewarsa, jiragen saman yaki da marasa matuka sun kai hare-haren ne kan masana’antu da ma’adanar rokoki da sansanin ba da horo da ofisoshin soji a Gaza.
Isra’ila ta kuma tarwatsa hanyoyin karkashin kasa guda biyu, inji kakakin nata wanda kai harin na matakin farko ne.
Rikicin Isra’ilawa da Falasdinawa ya yi kamari
Rikici tsakanin Isra’ilawa da Falasdinawa ya ta’azzara a ’yan kwanakin nan.
A karshen mako ne daruruwan mutane suka ji rauni a mummunan rikici a Masallacin Kudus.
Kungiyar Hamas ta ba Isra’ila wa’adin daren Litinin ta janye ’yan sandanta da suka mamaye Masallacin da kuma unguwar Sheikh Jarrah a Urushalima.
Jim kadan bayan karewar wa’adin, aka rika samun rahotannin hare-haren rokoki masu yawa.
Wani mai magana da yawun Hamas ya ce luguden “sako” ne ga Isra’ila da kuma “martani ga laifuka da cin zarafin da ta yi wa Birnin Kudus.”
Ita ma Kungiyar Jihadin Islama a Gaza ta dauki alhakin hare-haren wanda a yammacin Litinin ’yan gwagwarmayar Falasdinawa suka fara harba rokoki kan Isra’ila.
Isra’ila ta mayar da martani
Daga nan Isra’ila ta yi ruwan bama-bamai a wasu yankuna a yankin Gaza.
Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce mutane 22 ne suka mutu, ciki har da yara tara.
Kakakin sojojin na Isra’ila ya ce suna sane da rahoton kuma ana ci gaba da bincikarsa.
An kashe ’yan gwagwarmayar Hamas takwas a cikin hare-haren Isra’ila, a cewar jaridar Jerusalem Post.