’Yan bindiga sun koma rayuwar hannu baka hannu kwarya saboda katse hanyoyin sadarwa da aka yi a jihohin Zamfara da Katsina.
A yayin da sojoji ke ci gaba da yi wa ’yan bindiga luguden wuta a jihohin biyu, Aminiya ta gano yadda rashin abinci da man fetur ya tasa ’yan bindiga a gaba, har suna neman a kawo musu hatsi ko dan kadan ne a fanshi mutanen da ke hannunsu.
- Katse layukan waya: Zamfarawa da Katsinawa Na Kaura Daga Gida
- Yadda ake hada baki da ’yan uwa a sace mutane a Zariya
Wakilimu a Katsina, Yusuf Tijjani ya shadai wa ‘Shirin Najeriya A Yau’ wanda Aminiya ke gabatarwa ta intanet, cewa, “A yankin Pauwa a Karamar Hukumar Kankara … ’Yan ta’addar kan zo su sa shinge, duk wanda ya zo wucewa da abin hawa su tare shi, da tiyo dinsu da galan, su zuki mai a wajensa, wanda hakan ke nuna tsananin da suka shiga na bukata.
“Wasu rahotannin da muke samu na cewa idan mutum na da kayan abinci ko da tiya-tiya ne na shinkafa, in ya kai musu (’yan bindigar) za su iya karba su sakar mishin wanda suka kama.”
-
Gwamnati ta rufe kofar tuba
Tun bayan kimanin mako guda da rufe layukan sadarwa da haramta wasu harkoki — ciki har da kayyade yanayin sayar da man fetur — da nufin kassara ’yan bindiga, Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ce ’yan bindiga sun ji wuya, sun aiko masa cewa suna neman su tuba a yi sulhu da su, amma ya ce sun riga sun makara, ya rufe kofar karbar tubansu.
Gwamnan, wanda a baya ya yi ta sulhu da su, ya shaiwa wa manema labarai a Fadar Shugaban Kasa ranar Alhamis cewa ya riga ya yi duk abin da ya kamata na ba ’yan bindiga damar su tuba su ajiye makamai, amma suka ki, daga su ha’inci gwamnati, sai su bijire.
“Sun yaudare mu, sun karya alkawuran da muka kulla da su. Da farko mun yi tunanin ci gaba da sulhun, amma da muka lura ha’intar mu kawai suke yi, shi ne muka janye mu yake su har sai mun ga bayansu.”
Gwaman ya kara da cewa matakan da ake dauka na haifar da kyawawan sakamako.
“Saninku ne cewa muna yakar su kuma mun dauki matakai da dama na dakile su, Alhamdulillahi muna ganin haske kuma mun samu nasarori.
“Kamar yadda kuka sani, an girke jami’an tsaro da dama a Zamfara kuma suna aiki kan jiki, kan karfi,” inji shi.
A cewarsa, duk da cewa matakan da aka dauka da na tsauri, jama’ar jihar ba su damu ba sosai saboda yanzu suna jin kansu a cikin aminci.
A makon jiya, gwamnatin Jihar ta ce ta kama motocin jigilar abincin ’yan bindiga da wasu mutum kimanin 100 masu saba dokar haramcin da ta sanya wa wasu harkoki a sassan jihar.
-
Yadda rayuwar jama’ar gari ta koma
A yayin da sojoji ke ci gaba da farautar ’yan bindiga, wakilinmu a Katsina, Yusuf Tijjani, ya ce ana ci gaba da gudanar da harkokin banki a yankunan da aka rufe layukan sadarwar.
“Mu’amalar banki har yanzu tana faruwa, sai dai ‘alert’ ne in ka cire kudinka ko ka tura kudi ba za ka gani ba. Amma za ka iya shiga banki ka yi mu’amala.”
Amma ya ce duk da haka “Mutanen da ke wadannan wurare su ma suna dandana tasu kudar… Sun nuna cewa ba sa iya tuntubar iyalansu, ko su iyalan nasu su tuntube su, idan bukatar hakan ta taso.”
-
– Neman layin sadarwa
Hakan ta sa wasu daga Jihohin Zamfara da Katsina yin takakkiya zuwa Zariya a Jihar Kaduna domin su samu yin waya da abokan kasuwancinsu ko danginsu.
Wakilimu Aliyu Babankarfi, ya tattauna da wasu Zamfarawa da Katsinawa da suka je Zariya domin su samu su yi waya.
Ya yi kicibus da wani da ya zo daga yankin Jangebe, a Karamar Hukumar Mafara ta Jihar Zamfara, Musa Abubakar, wanda ya shaida masa cewa, “Yanke sabis din da aka yi ana samun sauki a-kai-a-kai a kan masu bayar da bayanai da wadannan barayin.
“Amma gaskiya yanke sabis da aka yi wasu abubuwa sun tsaya, amma tunda gyara za a yi, tsakani da Allah in dai haka za a yi to za a samu sauki, amma yankewar da aka yi, an rage wasu huldodi na musamman na rayuwa.”
Isa Usman ya ce musamman ya zo Zariya ne daga Kauran Namoda a Jihar Zamfara.
“Na zauna nan bakin ‘flyover’ saboda harkokin da muke yi da abokan kasuwanci na a Legas, ba zan same su ba, kwana biyu zan neme su, za su neme ni, ba za su same ni ba.
“A nan nake zaune duk abin da ya dace mu yi, mu yi, in kira su maganar kasuwanci da sauransu.”
Wani Direba daga garin Dutsin-Ma a Jihar Katsina, Alhassan Salisu, ya ce yanzu sun daina karbar sakonnin mutane, “Saboda in ka karba ma ba yadda za ka yi magana da wanda za ka ba a can.
“Ba ka san wanda za ka ba wa ba, kuma wanda za ka kira a waya ya karbi sakon ba yadda za ka kira shi.”