✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Halin da iyalai ke ciki bayan mutuwar magidanta a hastarin kwalekwalen ’yan Maulidi

An gano ƙarin gawarwakin ’yan Maulidin da suka rasu

’Yan uwan fasinjojin jirgin ruwan da ya kife da mutane sama da 300 a Jihar Neja sun bayyana yadda abin ya shafi rayuwarsu.

Mamatan, waɗanda ke hanyarsu ta zuwa taron Maulidi sun haɗu da ajalinsu ne ranar Talata da misalin karfe 8 na dare.

Duk da cewa lamarin ya faru ne a Jihar Neja, amma yawancin mutanen sun fito ne daga yankin Gbajibo ne da ke a Jihar Kwara.

‘Na rasa ’yan uwa bakwai’

Wani dan garin mai suna Honorabul Mahmud Salihu Gbajibo ya ce, “Babana shi ne ya assasa garin, Mudi Gbajibo, a Jihar Kwara.

“Na rasa mutane bakwai a cikin iyalina, ’ya’yansu biyu masu aure, ’ya’yana uku da kannena biyu a cikin goma sha daya da suka zo bikin suna.

“Ya kamata a yi bikin tun da farko amma na jinkirta shi saboda ina Ilorin a lokacin.

“Yawancinmu mun kaɗu da mutuwar ’yan uwanmu, amma dole muka binne su a Neja don guje wa tashin hankali a gida a Kwara.

“Bayan faruwar lamarin, matanmu sun rika gudu tsirara a cikin al’umma.

Harkoki sun tsaya cak

“Yanzu kuma, babu abin da ke gudana a garin, babu shagon da ke buɗewa, ba kuma wanda ke dafa abinci. Ba za ku iya samun abin da za ku saya ba, yana da muni.

“Na’ibin babban limaminmu da ’ya’yansa uku da suka je wakiltan Iimaminmu sun rasu su ma,” inji shi.

Gbajibo wanda ke cikin waɗanda suka karbɓi tawagar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kwara, ya shaida wa wakilinmu cewa, akwai bukatar a taimaka wa al’umma da babura.

“Yawancin waɗanda abin ya shafa da ba za su hau kwalekwale ba idan muna da babura saboda akwai hanyoyin da ke kaiwa wurin. Don haka muna roƙon a ba mu babura.”

Adadin mamata ya ƙaru

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Danladi Salihu, ya ce an gano gawarwaki 96 tare da binne 53, amma har yanzu ba a iya tantance adadin da ya bayar ba.

Masunta da jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), sun ce sun sake gano ƙarin gawarwakin mutane 20 a cikin ruwa bayan hatsarin a Ƙaramar Hukumar Mokwa ta jihar.

Hakan ya kawo adadin mamatan zuwa 36 a hukumance, kamar yadda hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ta bayyana.

’Yan uwana 5 sun rasu

Wani ɗan uwan waɗanda abin ya shafa, Haruna Yahaya wanda ya rasa ’yan uwansa biyar ya ce, “Na rasa ’ya’ya uku, uba da kannena a lamarin.

“Akwai mutanen da muke wasa kuma muna yin abubuwa tare.

“Al’amarin ya faru ne cikin dare kuma ba za ka san cewa wani abu ya faru a can ba.

“Wani jirgin ruwa ne da ya ratsa ta wurin da ya zo ya sanar da al’umma.

“A makon da ya gabata, mutane uku ne suka nutse a ruwa a lokacin da suke tsallaka kogin.

“Akwai buƙatar samarwa da aiwatar da amfani da rigunan kariya da jirgin ruwa na zamani. Wannan jirgin ruwan na katako ne kuma tsoho,” inji shi.

A nasa ɓangaren, wani dan garin da ya so a sakaya sunansa ya ce jirgin ruwan ya rabe kashi biyu ne a tsakiyar ruwan saboda yawan lodi.

Ya ce, “Sama da mutane 100 ne suka rasa masu kula da su saboda yawancin waɗanda abin ya shafa iyaye ne maza.”

A halin da ake ciki, shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar Neja bisa hatsarin jirgin ruwa.