✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Halima Djimrao za ta jagoranci gabatar da shirin ‘Daga Laraba’

Aminiya za ta fara gabatar da sabon shirin da karfe 10 na safiyar Labara, 19 ga Mayu, 2021.

Kamfanin Media Trust Company Limited, masu buga jaridar Daily Trust da Amniya, ya bullo da wani sabon shirin Podcast  da harshen Hausa mai suna ‘Daga Laraba.’

Fitacciyar ’yar jarida kuma tsohuwar ma’aikaciyar Sashen Hausa na Muryar Amurka, , Halima Djimrao, ce za ta jagoranci gabatar da shirin ‘Daga Laraba’ wanda za a fara gabatarwa daga ranar Laraba, 19 ga Mayu, 2021 da karfe 10 na safe.

‘Daga Laraba’ zai rika zuwa ne a kafafen sadarwa na zamani da kuma tashar rediyo ta TuneIn, a duk ranar Laraba da karfe 10 na safe.

Shirin zai mai da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka shafi kasa, ta hanyar tattaunawa da masana da za su yin fashin-baki game da tasirin abubuwa, sannan uwa uba ya samar da mafita.

Bullo da shirin podcast din da kuma takwaransa na Ingilishi (The Bearing, wanda za a fara daga ranar 22 ga Mayu 2021), na daga cikin hanyoyin da kamfanin Media Trust Limited ke bi domin inganta aikinsa da kuma biyan bukatun abokan huldarsa daidai da zamani.

Babban Editan Media Trust, Naziru Mikail, ya ce, “Sabon shirin na daga cikin kokarinmu na bunkasa shirye-shiryenmu ga masu sauraro a kafofin watsa labarai na zamani.

“Muna so mu ba su damar yin tsokaci ko shigowa cikin shiri kai tsaye don tafka muhawara kan matsalolin da suka shafi kasar nan.”

A yayin shirin masu sauraro za su samu ingantattun labarai daga sahihiya kuma amintacciyar kafa ta Daily Trust da Aminiya kamar yadda suka saba.

Tun bayan kafa Kamfanin Media Trust a 1998, suna buga jarida da sauran abubuwan da suka shafi aikin jarida, sannan ana iya samun labaransu a kafafen sada zumunta irinsu Facebook, YouTube, Twitter da kuma Instagram.