Daga hudubar Sheikh Aliyu bn Abdurrahman Alhuzaifi,
Masallacin Annabi, Madina
Huduba ta farko
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya halicci halittu kuma Ya kaddara musu abincinsu, ya iyakance ajalolinsu ba za su mutu ba har sai sun gama cin arzikinsu da kaiwa ajalinsu. Ina gode maSa Ma’abucin tsarki, ina tuba gare Shi, ina neman gafararaSa, wanda Ya nuna hanya Ya haskaka tafarki, har zukata suka ga gaskiya suka amsa wa kiran UbangijinSu, wasu zukatan kuma suka bace, suka fifita sha’awoyinsu suka mika musu wuya. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wanda ba Ya da abokin tarayya, shaidawa ta gaskiya da yakini, bisa imani da hakikaninta da aiki don cimma muradunta. Kuma na shaida Shugabanmu kuma Annabinmu Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa, wanda aka aiko da shiriya da addinin gaskiya, kuma da binsa ne zukata suke kaiwa ga burinsu a Lahirarsu da duniyarsu. Tsira da Aminci da Albarkar Allah su kara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa mafiya alherin al’umma, mafiya tsarki da da’a da takawa da sauran wadanda suka bi bayansu da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, ku ji tsoron Allah Madaukaki, ku yi maSa da’a, domin yi maSa da’a ne mafi tsayuwa da karfin aiki, ku yi guzuri da takawa domin Lahirarku. Ku sani lallai bayi suna samun fiffiko ne a wajen Ubangijinsu ta hanyar riko da addini da kyawawan dabi’u da gaskiya, kamar yadda Allah Madaukaki Ya ce, “Kuma ga kowane nau’i, yana da darajoji daga abin da suka aikata.” (k: 49:19). Sannan ya zo cikin wani Hadisin kudusi, inda Allah Madaukaki Yake cewa: “Yaku bayiNa! Iyaka ayyukanku ne nake lissafo muku, sannan in ba ku lada a kansu, don haka duk wanda ya samu alheri, sai ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa sai kansa.”
Ya ku Muslumi! Lallai dabi’ar hakuri dabi’a ce da siffa mai girma. Allah Ya siffanta Annabawa da Manzanni da Salihan bayi da ita, inda Yake cewa: “Saboda haka ka yi hakuri kamar yadda masu karfin niyya daga Manzanni suka yi hakuri.” (k: 49:35) da kuma fadinSa: “Kuma da Isma’ila da Idrisa da Zulkifili, dukkansu suna daga cikin masu hakuri.” (k: 21:85) da kuma fadinSa Madaukaki: “Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai. Wadanda suke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita da masu hakuri a kan abin da ya same su…” (k: 22:34-35).
Daga Anas -marfu’i- cewa Manzon Allah (SAW) ya ce, “Imani yanki biyu ne: yanki guda hakuri, daya yankin kuma godiya.” Muslim ya ruwaito. Shi kuwa Abu Malik Al’Ash’ari cewa ya yi: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Tsarki wani yanki ne na imani, kuma fadin Alhamdu lillahi yana cika mizani, sannan fadin Subhanallahi wal hamdulillahi suna cikawa-ko suna cika- abin da tsakanin sama da kasa. Sallah kuma haske ce, sadaka kuma dalili ne, sannan hakuri haske ne, kuma Alkur’ani hujja ne gare ka ko a kanka.” Ayoyi da hadisai kan hakuri da falalarsa suna da yawa kuma sun shahara.
Ma’anar hakuri shi ne a daure zuciya ga aikin da’a da kange ta daga aikata sabo a kowane lokaci da sanya ta ta rika yi wa Allah Madaukaki da’a a koyaushe.
Ya ku Muminai! Lallai hakuri yana da nau’o’i masu lizimtar juna, kuma daga mafiya girman nau’o’in hakuri, akwai hakuri daga barin aikata sabo da abubuwan da aka haramta. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma wadanda suka yi hakuri domin neman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da Sallah, suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi a asirce da bayyane, kuma suna tunkude mummunan aiki da mai kyau. Wadancan suna da akibar gida mai kyau (kyakkyawar makoma).” (k: 13:22).
Mafi yawan mutane sukan iya aikata ayyukan da’a, su yi hakuri a kan haka, amma ba za su iya hakuri daga aikata sabo ba, saboda haka wanda ke da karancin hakuri daga aikata haram ba zai kasance daga cikin masu hakuri ba, ba zai samu darajar mujahidai masu hakuri ba, domin babu mai kubuta daga fisge-fisgen sha’awoyi, sai mai hakurin gaske, mai tsentseni na hakika. Duk Musulmin da ya zamo bai siffantuwa da hakuri, to, wani lokaci zai zo da jin dadi na kusa ko wani dan amfani na kusa ko sha’awa mai wucewa ko wata kaba’ira mai halakarwa sai azamarsa ta gaza, iradarsa ta yi rauni, hakurinsa ya yi siriri ya dulmiya ga haram ya fada cikin halaka, ya zama shakiyyi babba, ya fada a azaba mai radadi!
Hakuri daga aikata haram kamar taya ce a jikin mota, ka suranta yadda mota za ta kasance idan babu taya, yaya makomarta zai kasance? Yaya kimarta zai zamo? Don haka idan hakuri da imanin mutum ba su kange shi daga aikata haram ba, to makomarsa a duniya kaskanci ne ko kurkuku, a Lahira kuma Jahannama, tir da wannan makoma, koda kuwa mutum yana ganin ya samu rabo da girma a wannan duniya!
Nau’i na biyu na hakuri shi ne: Hakuri a kan yi wa Allah da’a ta hanyar yin aikin da Ya ce a yi da yin sa daidai da yadda Ya ce a yi, da kuma hakurin dawwama a kansa. Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ka bauta wa Ubanginjinka, har mutuwa ta zo maka.” (k:15:99), sai kuma fadinSa: “Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi hakuri kuma ku yi dauriya kuma ku yi zaman dako, kuma ku yi takawa, tsammaninku za ku ci nasara.” (k:3:200).
Hasanul Basri (Rahimahullahu) ya ce, “An umarce su da su yi hakuri a kan addininsu da Allah Ya yardar musu da shi, shi ne Musulunci. Kada su bar shi saboda yalwa ko kunci, ko tsanani ko wadata har sai sun mutu suna Musulmi. Kuma an umurce su da su daure wa abokan gaba da suke kin addininsu.” Zaman dako shi ne dauwama a wurin ibada da tsayuwa kan umarnin Allah kada a tozarta shi.
Muslim ya ruwaito daga Hadisin Abu Huraira (RA) daga Annabi (SAW) ya ce, “Shin ba zan ba ku labari kan abin da Allah Yake shafe laifuffuka kuma Ya daukaka daraja da shi ba? Shi ne kyautata alwala a wuraren da ake ki (lokacin tsananin sanyi) da yawaita taku zuwa masallatai da jiran Sallah bayan Sallah, wannan shi ne zaman dakonku! Wannan shi ne zaman dakonku! Wannan shi ne zaman dakonku!”
Nau’i na uku na hakuri shi ne: Hakuri bisa kaddara da hakuri bisa masifu da abubuwan ki da suke samun bayi a wannan duniya. Wannan hakuri ba ya zama abin godiya sai ya zamo tare da tsammanin lada da kuma neman yardar Allah Madaukaki. Kuma ya zamo bawa ya san masifar abar kaddarawa ce daga Allah, kuma duk wanda ya yi hakurin za a ba shi lada, domin Allah Mai gudanar da al’amarinSa ne, wanda kuma ya rika kara har ya fusatar da Allah, sai ya yi laifi kuma al’amarin Allah Mai gudana ne. Allah Madaukaki Ya ce, “Kuma lallai ne muna jarraba ku da wani abu daga tsoro da yunwa da nakasa daga dukiya da rayuka da ’ya’yan itace, kuma ka yi bushara ga masu hakuri. Wadanda suke idan wata masifa ta same su, sai su ce, “Lallai mu ga Allah muke, kuma zuwa gare Shi masu komawa ne. Wadannan akwai albarku a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma wadannan su ne shiryayyu.” (k: 2: 155 -157).
An karbo daga Anas (RA) ya ce, “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Idan Allah Ya nufi bawanSa da alheri sai Ya gaggauto masa da ukuba a duniya, idan kuma Ya nufi bawanSa da sharri sai ya kyale shi da zunubinsa har sai ya saka masa da shi Ranar kiyama.
Ku sani girman sakamako yana tare da babban bala’i, kuma idan Allah Ya so mutane sai Ya jarrabe su da bala’i, wanda ya yarda, to, yana da yarda (daga Allah), wanda ya yi fushi, yana da (sakamakon) fushi (daga Allah)” Tirmizi ya ruwaito shi, kuma ya ce, “Hadisin ne mai kyau.”
Hakika Allah Ya yi umarni da hakuri marar iyaka cikin fadinSa “Kuma ka yi hakuri kuma hakurinka bai zama ba, face domin Allah” (k: 16: 127), sannan Ya yi umarni da hakuri a al’amura kebantattu saboda tsananin bukatar yin hakuri a cikinsu, sai Ya yi umarni da hakuri da hukuncin Allah shari’antacce da mukaddari, sai Ya ce, “Saboda haka ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi daga cikinsu mai zunubi ko mai kafirci.” (k: 76: 24). Kuma Ya yi umarni da hakuri bisa cutarwar kafirai, sai Madaukaki Ya ce: “Lallai ne za a jarraba ku a cikin dukiyarku da rayukanku, kuma lallai ne kuna jin cutarwa mai yawa daga wadanda aka bai wa Littafi a gabaninku da kuma wadanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi hakuri kuma kuka yi takawa, to, lallai ne wannan yana daga cikin manyan al’amura.” (k: 3: 186).