✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haka ta cimma ruwa

Yanzu abin nema ya samu wai matar makadi ta haifi kalangu. Hankoron da talakawan Najeriya suka dade suna yi don kawo canji a harkokin mulki…

Yanzu abin nema ya samu wai matar makadi ta haifi kalangu. Hankoron da talakawan Najeriya suka dade suna yi don kawo canji a harkokin mulki da na siyasa da kuma na zamantakewa ya tattaba a sakamakon zaben da aka gabatar a ranar Asabar. Wannan shi ne zaben da aka yi mafi inganci, daga cikin guda goma tun daga shekarar 1959 ya zuwa wannan karon, wanda aka kammala ba tare da an kai ruwa rana ba. Hakan ya kuma kwantar da hankulan jama’a domin sun tabbatar da cewa an ba su Janar Muhammadu Buhari domin kuwa shi ne suka zaba, ba kamar a lokutan baya ba, inda ake ta yin murdiyar da ta sha tayar da zaune tsaye.

Ingancin wannan zaben kuwa ya ta’allaka ne bisa kyakkyawan tsarin da aka yi ne wanda ya biyo bayan koke-koken talakawa game da yadda ake gudanar da zabe bisa son zuciyar shugabanni da kuma karya dukkan ka’idoji da dokokin kasa wajen daurewa shugaban da ke bisa mulki gindin zarcewa. Daga cikin wadannan koke-koken akwai wadanda Janar Muhammadu Buhari ya yi a gaban alkalan kotuna har sau uku bayan muzgunawa da aka yi masa lokacin da ya tsaya takara, amma babu wanda ya share masa hawaye. Sai daga bisani ne aka fahimci manufarsa na zuwa kotu, watau don neman a kyautata hanyoyin gudanar da zabe da kuma tottoshe dukkan kafafen da za a iya kurdawa a tafka magudi. Alhamdulillahi a wannan karon an gano haka, an kuma dauki matakan yin gyararrakin da suka kai ga biyan bukata.
Dangane da haka ne aka samar da wasu sababbin dabarun yin amfani da katin zabe na din-din-din da kuma wata na’urar tantance sahihancin katin da kuma nasabarsa da mai rike da shi don a magance hanyoyin magudi da kuma aringizon kuri’u. A bana wadannan dabarun sun taimaka ainun wajen magance kusan dukkan matsalolin da ke hana zabe yin armashi, domin kuwa sun hana yin magudi har hakan ya sanya aka yi zaben da ya fi kowanne inganci da kuma nagarta, ba tare da samun matsalolin da ke kawo yamutsi ko tunzuri ba a tashoshin jefa kuri’a. Wannan ne ya sa zaben bana ya zame tamkar wasa da macijin tsumma, ‘yan kallo lafiya mai wasan ma lafiya.
Muhimmancin wannan zabe ya sa kasashen duniya mayar da hankalinsu ga Najeriya, kasar da ake kallonta a matsayin giwar Afirka, kuma manya-manyan kungiyoyin duniya da kasashen da ke mu’amala da huldar arziki da Najeriya sun turo wakilan da suka sanya idanu kan yadda za a gudanar da zaben, don su kuma fahimci irin take-take da halayyar shugabanni da ‘yan siyasar Najeriya a lokutan gudanar da zaben. Tun kafin kawo karshen zaben wadannan manyan bakin suke ta yabawa da ingancin tsare-tsaren da aka yi, suna kuma kwanzarta kyawawan halayen da jama’a suka gwada, da kuma yadda suka gujewa abubuwan da za su iya tayar da zaune tsaye.
Ta haka ne aka samu nasara a zaben da ya gabata, kuma a karo na farko a tarihin siyasar Najeriya, an kifar da shugaban da ke bisa mulki, sa’annan shi ma ya shiga tarihi domin kasancewarsa shugaba na farko da ya yi kyawun kai, ya buga wayar tangaraho ga abokin hamayyarsa don taya shi murnar lashe zaben. Hakan ya nuna wa magoya bayansa masu hankoron tayar da fitina idan an kayar da shi cewa zabe fa ba gasa ne ba na a mutu-ko-a-yi-rai, ra’ayi ne na jama’a da suke nunawa ba tare da kuntatawa ko wani matsi ba, saboda haka nan wajibi ne a amince da hukuncin da suka yanke.
Koda yake a wannan karon ma ‘yan Najeriya sun nuna bangaranci da wasu ra’ayoyin da suka dade suna rarraba kawunan ‘yan Najeriya, amma duk da haka nan dai an yi wasu abubuwan da a lokutan baya ba a taba yin irinsu ba. Hadin kai tsakanin al’ummomin Kudu-maso-Yamma da kuma na Arewaci wani sabon abu ne da ya kara wa siyasar Najeriya armashi ainun, kuma idan haka ya ci gaba da dorewa bisa ga tsarin sabuwar jam’iyyar APC da suka samar tsakaninsu to ba shakka za a dawo daga rakiyar bakar siyasar da ta shiga tsakanin al’ummomin wadannan yankunan, kuma hakan zai kara karfafa matsayin sabuwar jami’iyyar da suka bi ta kanta suka kai ga nasarar kafa gwamnati, domin kuwa za ta ci gaba da mamaye dukkan lunguna da sako-sakon kasar nan.
To a nan sai mu yi kira ga sabuwar gwamnatin da Janar Muhammadu Buhari zai kafa da ta yi la’akari da abubuwan da suka wanzu a cikin shekaru goma sha shida da jam’iyyar PDP ta yi, tana gasa wa talakawan Najeriya aya a hannu, ta kuma yi taka-tsantsan wajen gudanar da kyawawan manufofin da take nuna wa jama’a har suka amince da ita, don kawar da su ko kuma magance su don amfanin jama’a. Muhimman ayyukan da gwamnatin Buhari za ta sanya a gaba su ne kawar da rashawa da cin hanci don al’amura su daidaitu bisa sahihin tafarkin farfado da martabar kasar nan da kuma habaka masana’antu da aikin gona don raba matasa, har ma da magidanta, da rashin aikin yi da kuma tabbatar da cewa albashin da ake ba wa ma’aikaci yana isarsa biyan dukkan bukatunsa ba tare da shiga wata hanyar cuwa-cuwa ko yin tumasancin da zai zubar masa da mutunci ba kafin ya samu na rufin asiri.
Ya kamata talaka ya yi tilawar ilmin-karbi-a-jika da ya yi na tsawon shekaru goma sha shida, ya kuma ci gaba da yin addu’ar da ya dade yana yi ta neman canji, ga Janar Muhammadu Buhari don Allah ya agaza masa, talakawan kasar nan kuma su kasance masu ladabi a gare shi da yin biyayya ga dukkan manufofin da ya tsara, ya gabatar. To, tunda dai hakar talakawa ta cimma ruwa a halin yanzu, kada su yarda su ci gaba da fama da kishir ruwa. Hanya guda ta yin haka ita ce ta ba Janar Buhari cikakken goyon bayan da suka saba ba shi don ya kai ga nasara da kuma samun sukunin sauke gagarumin nauyin da suka taru, suka dora masa.