Makonni biyu da suka gabata ne Hukumar Kula da Harkokin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta sanar da daukar matakin tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar Hajjin bana zuwa ranar 31 ga watan Janairun 2024.
Sanarwar ta ce, an dauki matakin ne bisa la’akari da damuwar da wasu malaman addini, hukumomin jin dadin alhazai na jihohi da gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar domin tsawaita wa’adin.
- Yadda sababbin hare-hare ke firgita mazauna Abuja
- Gawuna ya ɗauka zai ci banza kamar yadda Ganduje ya ci a 2019 — Kwankwaso
Haka kuma a wani labarin daban, Hukumar ta ce daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su koma kayyade farashin kujerar hajji ga maniyyata sabanin bai ɗaya da aka saba.
Hukumar ta yanke shawarar cewa a yanzu kowace jiha za ta kayyade farashinta bisa la’akari da wasu muhimman abubuwa na daiwainiya da alhazai kamar masauki da ciyarwa.
Shugaban NAHCON, Jalala Arabi ne ya bayyana hakan a jawabinsa yayin ganawarsa da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kuma hukumomi masu zaman kansu a birnin Makkah da ke Saudiyya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke tsaka mai wuya kasancewar har yanzu ba a cike kujerun da kasar take da su ba.
Nijeriya na da kujera 95,000 ne, daga ciki akwai guda 75,000 da aka ware domin maniyyata daga jihohi, sai 20,000 na musamman.
Binciken Aminiya domin gano yawan kujerun da suke rage bai cim ma ma ruwa, kasancewar jihohi ba su kammala turo wa hukumar alkaluma da kudaden wadanda suka biya ba.
Yadda aka rika samun hauhawar farashin kujerar Hajji
Mafi karancin kudin kujerar Hajji shi ne Dala 6,000, wanda karyewar darajar Naira ta sa kudin ya kara sama a Nijeriya.
Hakan ya sa Hukumar NAHCON ta umarci ’yan Nijeriya da su fara ajiye Naira miliyan 4.5 kafin a sanar da asalin farashin na karshe.
Binciken Aminiya ya nuna cewa, farashin kujerar ya hau da kashi 600 a tsakanin shekarar 2013 zuwa bara.
A 2013, ana biyan Naira N639,498 ne, har ya kai Miliyan 1.5 a 2020. A 2023 Naira miliyan 3 aka biya, sannan duba da yadda Dala ta kai Naira 841, farashin zai iya kaiwa Naira miliyan 5 ko 5.1.
Aminiya ta tattauna da shugabannin shirye-shiryen Hajjin bana na wasu jihohi, inda suka bayyana cewa, akwai wawakeken gibi.
A Jihar Kwara da Neja da Nasarawa sun bayyana cewa ba su samu cike kujerun da aka ware musu ba.
A Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu Danbappa, Darakta Janar na Hukumar a tattaunawarsa da Aminiya ya danganta rashin samun isassun maniyyata da tashin farashin Dala a kan Naira.
“A gaskiya wannan karin kudi da aka samu na kujera a bana ya yi yawa ne saboda halin da kasar ke ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kuma tashin farashin Dalar Amurka.
“Idan an duba dukkanin abubuwan da ake yi a aikin Hajji tun daga kan su biza da kudin masauki da na abinci da na zirga-zirgar alhazai a kasa mai tsarki duka da Dalar Amurka ake biya.
“Abin da ake iya yin sa da kudinmu bai wuce kudin sayen kayan sakawa da jaka da sauransu ba.”
Abin da maniyyata suke cewa
Aminiya ta tattuana da wasu daga cikin maniyyata a Jihar Kano, inda suka nuna cewa, idan har gwamnati ba ta yi wani kokari na rage farashin kujerar ba, to babu shakka aikin Hajji zai gagari mai karamin karfi.
“Duk da cewar aikin Hajji dama sai mai hali, amma saboda muhimmancinsa ga Musulmi, talaka ma yana iya kokarinsa wajen ganin ya samu tafiya.
“Kin ga a da mukan dan yi adashin gata don sauke wannan babbar ibada, amma a bana abin yana neman gagarar talaka duba da yawan kudin da aka zuba wa kujerar,” in ji Malam Abdullahi.
Wani maniyyaci da Aminiya ta tattauna da shi mai suna Abdurrahman Adam ya bayyana cewa, ya yi niyyar biya wa kansa da mahaifiyarsa kudin Hajjin, amma duba da farashin kudin na bana hakan ba zai yiwu ba.
“Wallahi tun bara na so na biya mana ni da mahaifiyata, amma lamarin bai yiwu ba saboda rashin isassun kudi. Hakan ya sa na hakura, na ce sai bana.
“To ga shi yadda banar ma ta kasance kudin ya yi yawan da ba zai yiwu na biya ba. A da ina tunanin abin da bai wuce Naira miliyan shida ba, a yanzu kuma maganar sama da Naira miliyan 10 ake yi.
“To ka ga ina za a samu sauran cikon kudin. Don haka ni a yanzu na fasa zuwa zan bar mahaifiyata ta tafi. Idan Allah Ya nufa baɗi ni sai na tafi.”
Ita ma wata maniyyaciya da ta nemi a sakaya sunanta ta bayyana cewa, ta daɗe tana so ta tafi aikin Hajji, amma abin ya gagara saboda karin farashin da ake yi a duk shekara, “A gaskiya na daɗe ina son tafiya aikin Hajji.
“Shekaru biyu da suka gabata na so na tafi, amma tsadar kujera ta hana ni. A 2022 ban sami tafiya ba saboda matsalar karancin jirgi da aka samu a wannan shekarar.
“A bara kuma sai aka zo aka kara Naira dubu 500, hakan ya sa ban tafi ba saboda ba ni da cikon kudin.
“Ina tunanin bana zan tafi saboda na yi tunanin karin kudin ba zai taka kara ya karya ba. Amma ga mamakina sai ga kari har Naira miliyan ɗaya da rabi.
“Ba a ma san ainihin kudin ba, domin wannan kafin alkalami aka ce a ajiye.”
Hajiya Nafisa Tudun Yola ta shaida wa Aminiya cewa, “Babu shakka tsadar kudin kujerar Hajji a bana sai a hankali.
“Don haka ni a yanzu da a biya min kuɗin aikin Hajji gara a ba ni kuɗin na yi wani amfanin da su. Watakila zuwa baɗi abubuwa sun gyaru sai mutum ya biya, ya tafi.
“Amman babu shakka, aikin Hajji a bana sai masu ido da kwalli.”
Haka kuma wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan al’amuran aikin Hajji mai suna Serve the Pilgrims Initiative ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba wa hukumar jin dadin alhazai ta jihohin Nijeriya wani tallafin bashi, wanda za ta yi amfani da shi wajen biyan kujerun Hajjin jihohinsu, zuwa lokacin da maniyyata za su kammala biyan kudaden kujerunsu.
Kungiyar ta SPI ta bayyana cewa, canje-canjen da aka samu wajen shirin aikin Hajjin na bana yana da kyau, sai dai zai fi kyau idan da kasar Saudiyya za ta bi a hankali wajen aiwatar da su.
“Canje-canjen da hukumomin kasar Saudiyya suka yi dangane da aikin Hajji abu ne mai kyau.
“Sai dai da za a bi su a hankali, da abin zai fi kyau. Idan an duba yawancin ‘yan Nijeriya suna biyan kudin aikin Hajji ne bayan watan Ramadan, wato bayan kaka don haka akwai bukatar a daga musu kafa zuwa wannan lokacin’’.
A cewar shugaban kungiyar, Malam Yakubu Fagge, idan har kasar nan ba ta iya cike gurbin kujeru dubu 95 da kasar Saudiyya ta ba ta a bana ba, to hakan zai iya shafar rabon kujerun da za a ba kasar a baɗi.
Haka kuma kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta taimaka wa maniyyata wajen samun canjin Dalar Amurka a kan Naira 750 kamar yadda aka sanya a kasafin shekarar 2024, wanda kuma ’yan majalisa suka amince da shi.
Abin jira a gani shi ne a yanzu da Hukumar Aikin Hajji ta kasa ta tsawaita lokacin da za a biya kuɗin kujera ko za a samu karuwar masu biyan kuɗin aikin Hajji ko kuma a’a?.