✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda sababbin hare-hare ke firgita mazauna Abuja

Hare-haren da aka aiwatar da lokutansu

Mazauna yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja yanzu haka suna zaune cikin tashin hankali da fargaba sakamakon tabarbarewar tsaron da ya keto cikin Birnin Tarayyar inda lamarin ke dada ci gaba da kamari, kamar yadda rahotonnin da Aminiya ta tattaro suka nuna.

Hatta kwaryar birnin bai tsira ba ta yadda masu satar motoci da ’yan fashi da makami da masu kwace da masu daukar fasinja a mota ko Keke-Napep su yi musu damfarar da aka fi sani da ‘One-Chance’ suke ci gaba da cin karensu ba babbaka.

Su ma yankunan talakawa masu karamin karfi da suke warwatse a yankuna shida na Abuja lamarin ya munana ta yadda mazauna yankunan suke fuskantar hare-hare daga ’yan bindiga da ’yan fashi da makami da masu sata da yin garkuwa da mutane.

Aminiya ta gano cewa a bara an kashe mutanen da ba su gaza 36 ba, kuma an sace mutum 339 a wurare daban-daban a yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Yankunan da abin ya fi shafa sun hada da Abaji da Bwari da Kuje da kuma Kwali. Sai kuma nan da can da akan samu irin wannan matsala a wasu kauyukan yankin Gwagwalada da yankin Binrin Abuja (AMAC).

Lamarin ya tilasta wa mazauna kauyuka da dama barin gidajensu zuwa wasu wurare saboda tsoron ta’asar maharan.

Kididdigar Aminiya ta nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2023 an kashe mutum 11 a Kuje; 7 a Bwari da Birnin Abuja; 5 a Kwali; sai 3 a kowane daga yanki na Abaji da Gwagwalada.

Wadannan alkaluma ne na wadanda aka samu labari a kai, domin mazauna yankunan sun tabbatar da cewa adadin ya zarce abin da aka bayyana a kafafen yada labarai.

Mazauna yankunan sun ce yawancin bata-garin da suke kai hare-hare a Babban Birnin Tarayya ba tare da samun wata turjiyar a-zo-a gani ba, sukan fito ne daga jihohin da ’yan bindigar suka yi kaka-gida masu makwabtaka da Abuja.

Abaji na iyaka da Jihar Nasarawa da Kogi da Neja; Bwari ta hada iyaka da jihohin Neja da Kaduna; Kuje wadda ta fi manyan dazuka tana iyaka da Jihar Nasarawa.

Daraktan Kudi da Gudanarwa na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS) na Babban Birnin Tarayya, Ebele Molokwu, ya bayyana a hirarsa ta karshen shekara da manema labarai a watan Nuwamban da ya gabata cewa yankunan Bwari da Kuje da kuma Abaji ne yankunan da suka fi shiga tsanani da fuskantar garkuwa da mutane.

Shi ma bayan nada shi Ministan Babban Birnin Tarayya, Mista Nyesom Wike, ya sha alwashin magance matsalar tsaro ta hanyar wadata hukumomin tsaro da kayan aikin da za su iya bai wa yankin tsaro.

Mista Wike, ya bayyana a taron bitar Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa, Shiyyar Abuja da aka gudanar a shekarar 2023 cewa akwai sababbin tsare-tsare na zamani da hanyoyin lura da kuma dakile harkokin tsaro a Abuja da za a fara aiki da su.

Hare-haren da aka aiwatar da lokutansu

Hare-hare na baya-bayan nan da aka aiwatar a kauyukan yankin Bwari kadai an sace manoma, ciki har da mata da kananan yara fiye da 53 a ’yan makonnin da suka wuce.

A ranar 18 ga Nuwamban da ya gabata ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Yewuti da ke yankin Kwali inda suka kashe mutum daya tare da yin awon gaba da mutum takwas ciki har da mahaifin Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kwali wanda aka sako shi tare da mutum biyu bayan biyan kudin fansa da aka ce sun kai Naira miliyan biyar.

Domin tsoro da gudun ci gaba da kawo musu hari, mazauna kauyen sun tabbatar da kaurace wa yankunan zuwa inda suke ganin sun fi musu kwanciyar hankali.

Daya da cikinsu mai suna Shu’aibu Aliyu ya shaida wa daya daga cikin wakilanmu cewa tuni mata da yara suka yi hijira zuwa makwabtan garuruwan Awawa da ’Yangoji da cikin garin Kwali.

A ranar 20 ga Nuwamba wasu ’yan bindigar sun sace mata takwas a wata gona da ke kauyen Gwombe a Masarautar Gwargwada da ke Karamar Hukumar Kuje.

Wadanda aka sace a wannan samame an ce dukkansu matan aure ne da suke aiki a wata gona da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar.

A ranar 9 ga Disamban bara wasu ’yan bindiga sanye da kayan sojoji sun kai hari a garin Dei-Dei da ke hanyar Kubwa zuwa Zuba a Karamar Hukumar Bwari inda suka yi awon gaba da mutum 25 a wasu rukunan gidaje uku da misalin karfe 8.30 na dare.

A washegari kuma aka sake kai wani hari a kan Titin Arab da ke Kubwa nan ma aka yi awon gaba da mutum bakwai ciki har da kananan yara.

A ranar 13 ga Disamban 2023, ’yan bindiga sun mamayi kauyen Gbaupe inda suka tafi da yara biyu da matasa tara a bayan Rukunin Gidajen Aco da ke kan hanyar filin jirgin samaa Abuja.

Wani mazaunin kauyen mai suna Ishaya Musa, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:34 na dare inda maharan suka dirar musu da manyan bindigogi kirar AK-47.

Ya ce maharan sun shiga wasu gidaje biyu suka yi awon gaba da kananan yaran da ba su wuce shekara 9 zuwa 13 ba suna harba bindigogi.

Haka a ranar 16 ga Disamban Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya ta kama wasu mutum uku da ake zargi da fashi da makami da satar motoci a kwaryar Abuja.

A ranar 23 kuma a watan Disamban 2023, ’yan bindiga sun afka wa mutanen Garam da ke da tazarar tafiyar minti biyar kacal daga garin Bwari inda suka yi awon gaba da mutum 13 ciki har da Faston Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG).

Alex Kaura, wani mazaunin garin Gwaram, ya ce bayan maharan sun kai harin sun samu nasarar sace wasu yara biyu bayan sun shiga wani gida inda suka yi amfani da su wajen tursasa musu su nuna musu gidajen wadanda suke nema.

“Yayin da suka isa can sun kama dukkan mutanen gidan kuma a lokacin da suke barin gidan sun harbe wani malamin addinin Kirista da suka zo nema, wato Faston Cocin Redeemed Christian Church of God. Sun harbe shi ne a gaban matarsa da ’ya’yansa uku,” in ji shi.

Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun yi awon gaba da wadanda suka yi garkuwa da su zuwa maboyarsu a dajin da ke iyakar Bwari da Kagarko da ke Jihar Kaduna.

A ranar 28 ga Disamban a yankin Kuduru da ke Karamar Hukumar Bwari da ya hada iyaka da Garam da ke Karamar Hukumar Tafa da ke Jihar Neja an kai hari aka sace mutum 18.

Sai ranar 30 ga Disamban 2023 a kauyen Mawogi da ke Gundumar Gawu a Abaji inda maharan suka yi awon gaba da manoma takwas da misalin karfe 11:30 na dare, in ji wani mazaunin kauyen.

Sai ranar 1 ga Janairun sabuwar shekarar nan, ’yan bindigar sun kai samame a Barangoni da ke Bwari inda suka harbe wani dan sintiri sannan suka yi awon gaba da mutum uku.

A ranar Laraba 3 ga Janairun bana ’yan bindigar sun kashe mutum daya sannan suka yi awon gaba da iyalai bakwai a Zuma 1 da ke tsakiyar Gundumar Bwari.

Shedrack Samson, ya ce lokacin faruwar lamarin da misalin karfe 12:04 na dare an harbi ’yan sanda biyu da suka kai dauki inda suka samu raunuka.

A hirarsa da Aminiya, wani mai sarauta a Birnin Tarayya, Abuja da ya bukaci a sakaye sunansa, ya ce hare-haren manyan abubuwan takaici ne.

“Hatta a tarurrukan tsaro da muka yi da Ministan Abuja na bayar da shawarar a wadata ’yan sintiri da kayan aiki kuma a rika ba su wasu ’yan kudade a wata da za su rika samun kwarin gwiwar tunkarar ’yan bindigar, amma gwamnati kamar ta fi mayar da hankali ne kawai ga ’yan sanda,” in ji shi.

A ranar Alhamis 4 ga Janairun da muke ciki ’yan bindiga sun kai hari a kauyen Tekpeshe-Gurdi da ke Mazabar Gurdi a Karamar Hukumar Abaji inda suka tafi da mutum biyar.

Kansilan Mazabar Gurdi, Wozhe Ishaya, ya ce maharan sun rufe hanyar Tekpeshe-Gurdi inda suka tare masu dawowa daga garin Tekpeshe suka tafi da su.

Kwararru sun ba da mafita

A zantawar Aminiya da wani kwararre kan harkokin tsaro mai suna Abdulkarim Gazali ya yi kira ga gwamnati ta sa dokar ta-baci kan harkar tsaro a yankin Birnin Tarayya, Abuja.

Ya ce gwamnati tana jan kafa wajen biyan ma’aikatan tsaro a yankin Birnin Tarayya.

Sai ya bukaci Hukumar Birnin Tarayya ta kara yawan jami’an tsaro da za su rika yin aiki da mutanen gari.

“Bari in fada muku dalilin da ya sa ba zai yiwu a daina ta’addanci da sata da garkuwa da mutane a yankin Birnin Tarayya ba, mutane da dama ciki har da wasu manyan jami’ai da wasu sarakuna suna amfana daga matsalar tsaron,” in ji shi.

Biodun Ogunleye, wani kwararre kan harkar tsaro ya bayyana a wata hira da wakilinmu cewa: “Kyakkyawar hanyar da ta dace a bi don shawo kan matsalar, ita ce fara magance cin hanci da rashawa a bangaren tsaro domin akwai alaka da ta kut-da-kut tsakanin cin hanci da rashin tsaro.”

Sakataren Sashin Bayar da Umarni da Sa-Ido a sashen tsaro na Birnin Tarayya, Peter Olujimi, bai ce komai ga wakilinmu ba yayin da ya kira shi kan batun, kuma bai amsa sakon kar-takwana ba da daya daga cikin wakilanmu ya tura masa ba don jin ta bakin hukuma a kan lamarin.

’Yan sanda sun san jami’ansu masu motocin sulke a wuraren da suka dace

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Birnin Tarayya, ta ce rundunarsu ta sanya motocin sulke da jami’anta a wureren da suka dace don kara karfafa tsaro ga mazauna yankunan.

Kakakin, Josephine Ade ta bayyana wa wakilinmu ta wayar tarho cewa Kwamishinan ’Yan sanda, Haruna Garba, ya zagaya dukan wurarn da ke bukatar kara karfafa tsaro don kawo jami’ansu.

“Abin da muke taka-santsan da shi, shi ne bayyana hanyoyi da matakan da muke dauka don kada miyagu su yi amfani da shirin wajen shammatar lamarin kamar yadda suka saba,” in ji Adeh.