Tsohon babban hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Theophilus Y. Danjuma, (mai ritaya), ya ce ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta ya sa ƙasar ta zama abin dariya da abin kunya a idon duniya.
Janar Danjuma ya bayyana hakan ne a wannan Juma’ar yayin da yake jawabi a wajen bikin kamun kifi da al’adu na Nwonyo da aka saba gudanarwa duk shekara a Ƙaramar Hukumar Ibbi ta Jihar Taraba.
Ya ba da shawarar cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa don magance matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.
- Ƙiyayyar da ake yi wa ’yan sanda na shafar harkar tsaro a Nijeriya — PCRC
- An kashe sarki a fadarsa a Taraba
“Dole ne hukumomin Najeriya su ɗauki matakan gaggawa don ƙwato martabar ƙasar ta hanyar magance ƙalubalen tsaro da take fuskantar al’ummar ƙasar,” in ji shi.
Janar mai ritaya ya ci gaba da cewa, babu wani mutum musamman baƙi da zai yarda ya zo ƙasar don saka hannun jari ko ziyartar wuraren yawon buɗe ido idan ba a tabbatar da tsaro ba.
“Babu wani mutum ko ƙungiya da za su so zuwa jiharmu ko ƙasarmu idan muka ci gaba da kashe kanmu da yanka kanmu,” in ji shi.
Danjuma ya kuma koka da yadda ake fuskantar ƙalubalen tsaro a faɗin Najeriya, inda ya ƙara da cewa munanan lamarin na buƙatar kulawar gwamnati cikin gaggawa.
Ya roƙi cewa dole ne a haɗa hannu guda don samun manufa guda da ta dace.
Ya ce, “Dole ne masu riƙe da muƙamai su yi aiki tuƙuru don ganin ƙasar nan ta kasance lafiya ga dukkan ‘yan Najeriya ciki har da baƙi kafin mu samu ƙarin masu zuba jari a ƙasar.
“Idan muka ci gaba da barin hanyoyinmu babu tsaro ga jama’a da za su iya gudanar da harkokin su da yin zirga-zirga, burinmu na bikin kamun kifi da al’adu na Nwonyo ya zama bikin ƙasa da ƙasa, ba za a iya cimma burin ba.
“Abin takaici ne yadda Nijeriya a matsayin ƙasa dunƙulalliya ta zama abin dariya sakamakon ƙalubalen tsaro.
“Kamar yadda ƙasar take a halin yanzu, mun zama abin kunya a idon duniya baki ɗaya don haka dole ne mu farfaɗo da kimarmu mu gyara ƙasarmu saboda a yanzu mun zama abin dariya ga duk duniya,” in ji shi.