✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alhazai sama da 900 sun mutu a Hajjin Bana

Alhazai 550 sun rasu ne a dalilin tsananin zafin da ya kai maki 51.8 a kan ma’aunin Celcius.

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar cewa alhazai sama da 920 ne suka rasu a lokacin aikin Hajjin bana.

Mutum 550 da cikin mahajjatan sun rasu ne a dalilin tsananin zafin da ya kai maki 51.8 a kan ma’aunin Celcius.

Wata majiya ta ce, daga cikin mutanen da suka mutu, sama da 600 ’yan kasar Masar ne, 60 daga Jordan yayin da Iran ke da 5 daga cikin wadanda suka rasu a sakamakon cututtuka masu alaka da zafi.

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta  ce, mutum uku ne suka mutu a lokacin aikin Hajji, wanda hakan ya sa adadin mahajjatan Najeriya da suka mutu a Saudiyya ya kai 15.

Shugaban tawagar likitocin Najeriya a aikin Hajjin, Abubakar Adamu Ismail, ya ce alhazan kasar biyu masu juna biyu sun yi bari, wasu alhazan biyar sun samu bugun zuciya sannan wasu 25 suka samu karancin ruwa a jiki a sakamakon matsanancin zafi.

NAHCON ta sanar cewa ranar 22 ga watan ga watan nan na Yuni za a fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida, inda za fara da alhazan Jihar Kebbi.

Alhazan sun gudanar da aikin hajjin da tallafin hukumomin da ke raba musu kayayakin rage zafi da suka haɗa da ruwan sanyi, ice cream da sauransu.

A cewar Hukumomin ƙasar, sun bada shawara ga alhazai da su riƙa amfani da lema, da kuma guje wa shiga rana idan ta take, duk da yawancin ayyukan ibada na buƙatar tsawaitar lokaci.