✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hajjin 2024: Maniyyacin Kebbi ya rasu a Saudiyya

Mutumin ya rasu a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya.

Allah Ya yi wa wani mutum daga Jihar Kebbi rasuwa bayan ya sha fama da gajeriyar rashin lafiya a birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), ya rawaito cewa marigayin, Alhaji Muhammad Suleman, daga ƙaramar hukumar Argungu, ya rasu ne a ranar Lahadi bayan gajeriyar rashin lafiya.

Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruku Aliyu Enabo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Makka a ranar Lahadi.

Ya ce: “Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi bayan ya sha fama da gajeriyar rashin lafiya, kuma an yi jana’izarsa a masallacin harami.

“An yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a wannan rana.

“A madadin gwamnatin Kebbi, ina son miƙa saƙon ta’aziyyarmu ga iyalansa, alhazan Kebbi da ɗaukacin al’ummar jihar baki ɗaya.

“Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma jiƙansa da sauran Musulmin da suka rasu, Allah Ya sa Aljanna Firdausi ta zama makomarsu.”

Shugaban ya buƙaci iyalan marigayin da su yi masa addu’a, tare da nema masa gafara wajen mahaliccinsa.