✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Hajjin 2022: Saudiyya ta sake sassauta dokokin kariyar COVID-19

A iya masallacin Harami da masallacin Manzon Allah S.A.W ne kadai za a saka takunkumi.

Hukumomin kasar Saudiyya sun sassauta dokar yaki da cutar COVID-19 saboda saukaka wa maniyyata Aikin Hajjin bana, inda suka kawar da batun amfani da takunkumin rufe fuska.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da maniyyata kusan 850,000 suka fara isa kasar domin shirin Hajjin na bana.

Hukumomin sun ce daga yanzu, za a bukaci maniyyatan su saka takunkumin ne kawai a Masallacin Ka’aba da ke birnin Makkah da kuma Masallachin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.

Sanarwar hukumomin ta ce ban da wadannan wuraren ibada guda biyu, ba a bukatar maniyatan su yi amfani da takunkumin.

Ko a hajjin bara sai da maniyyata suka yi amfani da dokokin kariya daga cutar, wanda suka hada da sanya takunkumi, amfani da sinadarin wanke hannu da kuma bayar da tazara.

A 2020 ne lokacin da ake tsaka da annobar ta COVID-19, hukumomi a kasar Saudiyya suka bai wa mutum 1,000 kacal daga cikin kasar damar yin aikin hajji.