Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta umarci Hukumomin Kula da Jin Dadin Alhazai na Jihohi da su ci gaba da yi wa maniyyata rajista da kuma shirye-shiryen aikin Hajji da Umarah na 2021.
Kakakin NAHCON, Fatima Sanda, cikin wata sanarwa, ta ce ci gaba da zirga-zirgar jirage daga wasu kasashe da kasar Saudiyya ta yi ya ba da karin kwarin gwiwa cewa maniyyata za su samu damar sauke farali da kuma yin Umarah a bana.
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
- Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?
- Bayan shekara 100 Sarautar Zazzau ta koma gidan Mallawa
“Hukumar na kira ga maniyyata da kuma hukumomi da kamfanonin aikin hajji da su ci gaba da shirye-shirye da kuma yin rajistar maniyyata, sannan su yi hakuri su jira lokacin da Saudiyya za ta fitar da cikakken bayani,” inji Shugaban NAHCON, Zikrullah Kunke Hassan, a cikin sanarwar.
Shugaban Hukumar, ya ba wa maniyyatan Najeriya tabbaci cewa da zarar Saudiyya ta fitar da ka’idojin aikin Hajji da na Umarah, NAHCON za ta yi maza ta dauki matakan da suka dace domin biyan bukatar maniyyata.
Saudiyya ta dakatar da shigar jirage kasarta daga ketare sakamakon annobar COVID-19, lamarin da ya kai ga takaita yawan mahajjata zuwa 10,000 a shekarar 2020, sabanin fiye da miliyan biyu da ke sauke farali a duk shekara.