Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta daidata da kamfanonin jiragen sama hudu na cikin gida da aka ba wa kwangilar jigilar maniyyata a aikin Hajjin da ke tafe.
Bangarorin sun daidaita ne bayan a makon jiya kamfanonin sun ki sanya hannu kan yarjejeniar aikin saboda yakin kasar Sudan da ke bukatar su sauya hanyar jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya, lamarin da zai kara wa afiyar tsawo.
- Jirgin ruwa ya nutse da mutum 20 a Sakkwato
- Yadda ake sauraron karar Atiku kan nasarar Tinubu a zaben 2023
A kan haka ne wakilan kamfanonin suka ki sanya hannu kan yarjejeniyar aikin, bisa hujjar cewa karin sawon tafiyar zai kara yawan kudaden da za su kashe, don haka suka bukaci karin kudin jigilar maniyyatan.
Amma, shugaban hukumar, Hassan Zikrullah Hassan, ya ce, a zaman da aka sake yi ranar talata a ofishinn NAHCON da ke Abuja, kamfanonin — Aero Contractors da Air Peace da Azman Air da kuma Max Air — sun amince sun sanya hannu kan yarjejeniyar da suka ki amincewa da farko.