✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hafsoshin soji biyu sun rasu a harin ISWAP

Kyaftin da Laftanar da wasu sojoji sun kwanta dama a yayin a aka kashe mayakan ISWAP 16

Hafsohin sojin Najeriya biyu da wasu kanann sojoji shida sun kwanta dama a harin da kungiyar ISWAP ta kai a Jihar Borno.

A yayin harin, sojoji sun aika mayakan kungiyar akalla 16 lahira a musayar wutar da suka yi a garin Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno.

“A bin takaici wani mai mukamin Kyaftin da mai mukamin Laftanar da sojoji shida sun kwanta dama a yayin a aka kashe mayakan ISWAP 16 a musayar wutar,” a cewar wata majiyar tsaro.

Ta ce sojojin sun kuma lalata motocin ’yan ta’addar a harin na Rann da ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru.

Abin ya faru ne da misalin karfe 1.30 na dare kafin wayewar garin ranar Juma’a, a cewar majiyar.