Salihu Tanko Yakasai, hadimin Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana ta farko bayan dakatar da shi daga aiki saboda sukar shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Tanko Yakasai mai amsa inkiyar Dawisu, ya yi godiya ga dukkan mutanen da suka nuna goyon bayan a garesa bayan dakatarwa da Ubangidansa ya yi masa a ranar Lahadi.
Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter da misalin karfe 12.13 na ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, Dawisu ya yi godiya da jinjina gami da bayyana farin ciki ga dumbin al’ummar da suka ware lokaci suka aike masa da sakon goyon baya da jajanta masa a kan lamarin da ya faru.
“Ina son mika cikakkiyar godiyata ga duk wadanda suka nuna min goyon baya a jiya (Lahadi), musamman wadanda suka kira ni ta wayar salula ko suka aiko sakkonni ta kafofin sadarwa daban-daban da wadanda suka wallafa a shafukansu na dandalin sada zumunta.”
“Na yi iya bakin kokari domin na mayar da amsoshin sakonnin amma gaza wa bata bari nayi hakan ba, saboda haka tun daga cikin zuciyata ina mika godiyata a gareku.”
A Lahadin da ta gabata ne dai Ganduje cikin wata sanarwa da Kwamishinansa na labarai, Muhammad Garba ya raba wa manema labarai, ya dauki matakin dakatar da hadiminsa saboda wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter na nuna rashin ladabi ga Shugaban Kasa.
Sanarwar ta ce, “Duk da cewa Yakasai ya yi kalaman ne bisa bayyana ra’ayi na kashin kansa, sai dai yana da wahala jama’a su bambance hakan duba da matsayinsa na jami’i mai rike da mukamin gwamnati.