Rahotannin sun bayyana cewa wani mummunan hadarin mota ya yi ajalin wasu malaman da’awa shida a Jihar Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa malaman sun rasu ne a hadarin mota da rutsa da su a kan hanyarsu ta dawowa daga Karamar Hukumar Sumaila da ke Kanon.
- Buhari ya amince da bude kwalejojin fasaha a wasu jihohi uku
- Boko Haram da ’yan bindiga na aiki kafada da kafada — Lai Mohammed
Bayanai sun ce malaman suna kan hanyarsu ta dawowa ce daga yawon da’awa inda suka je musuluntar da maguzawa a Karamar Hukumar.
Wata majiya daga Imamu Malik Foundation, gidauniyar da a karkashinta ne malaman su ke zuwa da’awar, ta ce dukka malamai, shidan wadanda kuma su ne jagororin da’awar sun rasu.
Majiyar ta ce a safiyar ranar Laraba ce dai malaman, har ma da wasu daliban su, suka tafi Sumaila din domin musuluntar da maguzawa.
Sai dai majiyar ta ce ba su samu labarin cewa daliban sun rasu ko sun ji raunuka ba, amma ta tabbatar da cewa malaman duk sun rasu.
Ta ce Mallam Alkassim Zakariyya, wanda shi ne jagoran tafiyar, shi ma ya riga mu gidan gaskiya.
“Yanzu haka muna can Imamu Malik Foundation a unguwar Dakata, muna jiran sauran dalibai su karaso sai mu wuce gidan Sheikh Alkassim Zakariyya, inda a nan ne za a yi musu jana’iza,” a cewar majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta.
Sai dai kawo yanzu hukumomin tsaro na rundunar Kiyaye Hadurra da na rundunar ’yan sandan Kano ba su tabbatar da ingancin rahoton ba.