Akalla mutum 257 ne suka mutu a hadarin jirgin soji da ya faru a Arewacin Aljeriya, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na sojoji da ke Boufarik da ke Algiers babban birnin kasar da safiyar Laraba.
Akasarin wadanda suke cikin jirgin sojoji ne da kuma iyalansu, a cewar ma’aikatar tsaro kamar yadda BBC ta ruwaito. Sannan kuma akawai ma’aikatan jirgin sama 10 da suma suka mutu a cikin hadarin jirgin.
Kawo yanzu ba bu cikakken bayani akan abin da ya janyo hadarin jirgin saman.
Amma kafar talbijin ta kasar ta ce, motocin daukar marasa lafiya 14 sun isa wajen da lamarin ya afku inda aka dauki wadanda suka jikkata zuwa asibiti.
Hotunan wajen da lamarin da ya afku sun nuna yadda hayaki ke fitowa daga tarkacen jirgin a filin da jirgin da fado.
Wata sanarwa daga ma’aikatar tsaron kasar ta ce, shugaban rundunar sojin kasar, ya bayar da umarnin a gudanar da bincike a kan musabbabin afkuwar hadarin, inda kuma zai kai ziyara wajen.
Kafar yada labarai ta Algerie24, ta ruwaito cewa, fiye da sojoji 200 ne a cikin jirgin.
Yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutane da dama sun mutu a cikin jirgin.
Shekara hudu da suka gabata ma wani jirgi da ya dauki sojoji da iyalansu ya yi hadari a kasar ta Algeria, inda mutum 77 suka rasa rayukansu.
Ana dai yawan samun hadarin jirgin sama a kasashe da dama inda ake kuma asarar rayuka.
Ko a watan Fabrairun 2018 ma, wani jirgin sama ya fadi a yankin Zagros mai cike da tsaunuka a lardin Isfahan a lokacin da yake kan hanyarsa daga Tehran zuwa Yasuj da ke Kudu maso Yammacin Iran inda mutum 66 suka mutu.