✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi odar jiragen yaki 80

UAE za ta saji jiragen soji 92 a kan Yuro biliyan 17 daga kasar Faransa

Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta yi odar jiragen yaki 80 a kan Yuro biliyan 14 daga kasar Faransa.

Kasashen biyu sun rattaba hannu a kan takardun sayen jiragen yaki guda 80 kirar Rafale daga Faransa a kan Yuro biliyan 14, sannan UAE ta amince ta sayi helikwaftocin jigilar kayan yaki guda 12 kirar Cararal a kan Yuro biliyan 3 daga Faransa.

Gwamnatin Faransa ta ce, “Wannan shi ne abin da kawancen kasashen biyu ya haifar domin inganta karfinsu na yin aiki tare wajen tabbatar da tsaro da cin gashin kai.”

Kasashen biyu sun kulla cinikin ne bayan Yarima Mai Jiran Gado, Sheikh Mohammed bin Zayed, ya gana da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, wanda ke ziyarar aiki na kwana biyu a kasar.

Hadaddiyar Daular Larabawa, wadda ta fi kowa sayen makamai daga Faransa daga 2011 zuwa 2020 ta kuma yi alkawarin zuba jari a bangaren kasuwanci na Yuro biliyan takwas a Faransa.

Ita ma Gidauniyar Mubadala da ke Abu Dhabi a kasar, ta yi alkawarin zuba jarin Yuro biliyan takwas a harkokin kasuwancin kasar Faransa.

Wani rahoto da Majalisar Dokokin Faransa ya fitar ya nuna a cikin shekara 10 da suka gabata, UAE ta sayi kayan yaki na Yuro bilyan 4.7 daga kasar.