Kamar yadda aka saba, duk watan Janairu yakan zo wa ’yan wasa da masoya wasan kwallon kafa da sabon salo da tunani da shaukin sanin makomarsu.
Tuni aka fara hada-hadar kasuwancin ’yan wasan, inda da yawa daga cikinsu suka fara kaura zuwa wasu kungiyoyi, ko dai domin su samu damar baje kolin fasaharsu, ko kuma sun samu ci gaba daga karamar kungiya zuwa babba, ko kuma sun samu karin kudi.
Daga cikin manyan wadanda suka canja sheka a kasuwar ta bana akwai:
1. Albaro Morata: Daga Chelsea zuwa Atletico Madrid
Albaro Morata, fitaccen dan wasa ne da a lokuta da dama aka rika lissafawa a cikin wadanda za su iya maye gurbin Ronaldo da Messi idan sun gaji. Asalinsa dan wasan Real Madrid ne, amma saboda rashin buga wasa, sai ya koma kungiyar Jubentus a matsayin aro, inda a nan tauraronsa ya haska matuka har Madrid din ta ga ya dace da dawo da abinta. Amma kuma kash! Tun dawowansa ya rika samun koma-baya.
A shekarar 2017 ya koma Chelsea kan Fam miliyan 60 a yarjejeniyar kwantaragin shekara biyar. Amma kuma a cikin wasa 47 da ya buga, kwallaye 16 kawai ya zura, wanda hakan ya sa Chelsea ta tura shi Atletico Madrid a matsayin aro, ko hakan zai sa ya dawo kamar yadda yake a da.
2. Kebin-Prince Boateng: Daga Sassoulo zuwa Barcelona
A wani kasuwancin ’yan wasa mai kama da almara, Prince Boateng dan asalin kasar Ghana ne kungiyar Barcelona ta dauka a matsayin aro daga kungiyar Sassoulo da ke Italiya zuwa karshen kakar bana.
Abin mamakin shi ne ganin ya tsufa domin shekarunsa 31 yanzu sannan ga Barcelona tana da kwararrun ’yan wasan gaba. Sai dai kuma yana da kwarewa domin ya buga wa kungiyoyi kamar su AC Milan da Borussia Dortmund da Tottenham.
3. Gonzalo Higuain
Shi kuma dan wasan Jubentus, Gonzalo Higuain ya koma kungiyar Chelsea ce. Dama can yana kungiyar A C Milan a matsayin aro ne daga kungiyar Jubentus. Gonzalo Higuain dai fitaccen dan wasa gaba ne tun a lokacin da yake Real Madrid. Zuwan Cristiano Ronaldo ne ya sanya dole ya tafi A C Milan domin ya rika samun isasshen lokacin wasa.
4. Mikel Obi: Daga Tianjin Teda zuwa Middlesbrough
Kyaftin din Super Eagles, shi ma ya baro kasar China inda ya dawo Ingila da taka leda bayan kusan shekara biyu da barin kasar.
Mikel ya bar kungiyar Chelsea inda ya koma kulob din Tianjin Teda ta China, sannan bana ya dawo kulob din Middlesbrough da ke rukunin ’yan dagaji na kasar Ingila da taje neman zuwa rukunin Firimiya.
5. Mario Balotelli: Daga Nice zuwa Marseille
Dan wasan Italiya, Mario Balotelli ya koma Marseille da taka leda daga kulob din Nice, inda ya amine da kwantiragin zuwa karshen kakar bana.
Balotelli mai shekara 28 a duniya ya buga wa kulob din Inter Milan wasa, inda har ya lashe gasar Zakarun Turai, kuma ya buga wa Manchester City da Liberpool, sannan daga baya ya koma Nice ta Faransa domin ya farfado da kwallonsa.
Balotelli dai matashi ne wanda ko shakka babu ya iya taka leda, sai dai tsaurin kai da jawo cece-kuce suna kawo masa cikas.
6. Bictor Moses: Daga Chelsea zuwa Fenerbahce
Shi ma tsohon dan wasan Najeriya, Bictor Moses, ya koma kulob din Fenerbache na kasar Turkiyya domin samun damar buga wasa.
A kakar bara, Moses yana cikin manyan ’yan wasan Chelsea, amma kamar yadda Hausawa suke cewa, duniya juyi-juyi, tun bayan da mai horar da ’yan wasa, Sarri ya maye gurbin Conte, sai Moses ya koma dan zaman benci. Hakan ya sa ya yanke shawara tafiya Fernabache a matsayin aro.
7. Real Madrid ta taya Rashford Fam miliyan 100
A wani kasuwancin da ake neman kullawa, kulob din Real Madrid ya taya dan wasan Manchester United Marcos Rashford a kan Fam miliyan 100.
Madrid na neman dan wasan ne kasancewar har yanzu bai amince da sabunta kwantiraginsa ba. Amma rahotanni suna cewa Manchester United na neman sabunta masa kwantiragi, inda za su rika biyansa Fam dubu 200 duk mako.