Tsakanin ranakun Litinin da Talata 3 da 4 ga watan Disamban nan biyu daga cikin shugabannin jam’iyyar adawa ta PDP da kuma na jam’iyyar da take mulki wato APC, a wurare daban-daban sun yi wasu kalamai da sunan gangamin neman kuri’a da ake kai yanzu a kasar nan kasancewar zabubbuka sai kara karatowa suke yi. Kalaman za a iya fassarasu da kalaman nuna kiyayya da mahukuntan kasar nan suke ta kamfen din lallai ya kamata a daina su, kasancewar sukan iya rura wutar rikice-rikice da rashin zaman lafiya da ya yi karanci a kasar nan a ’yan shekarun nan.
Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato kuma jigo a babbar Jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa aka fara ji a ranar Litinin 3 ga Disamba yana furta wasu kalamai masu kama da na kiyayya a Sakkwato birnin Shehu, lokacin kaddamar da gangamin neman kuri’a na dan takararsu na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a Shiyyar Arewa maso Yamma da ta kunshi jihohin Sakkwato da Katsina da Kebbi da Kano da Kaduna da Jigawa da Zamfara. An ji shi yana cewa takarar neman Shugabancin Kasar nan a shekarar 2019, za ta kasance ne tsakanin mai tallar tsiya da mai tallar arziki, don haka a fadarsa ya rage ga masu zabe su zabi mai arziki ko matsiyaci.
Bisa ga irin yadda ya ga dafifin dubban jama’ar da suka halarci taron, tsohon Gwamnan na Sakkwato, ya kasa boye shaukinsa, har sai da ya ce “Amma mutanen shiyyar Arewa maso Yamma kun fitar da mu kunya, kun nuna akwai PDP a wannan shiyya. Mutum biyu ke tafiya, da mai tallar arziki da mai tallar tsiya. Wa za ku zaba? Mai arziki ko matsiyaci.” Da yake mayar da martani a kan masu cewa ba za su zabi PDP da dan takararta na neman Shugaban Kasa ba, Alhaji Attahiru, ya fadi cewa sun dai san cewa ba mai ba da mulki sai Allah, don haka da yardarSa dan takararsu Alhaji Atiku, zai samu nasara, kuma PDP, za ta yi nasara daga sama har kasa.
A kashegarin Litinin, wato Talata 4 ga Disamba, yayin da yake gabatar da jawabinsa mai karatu ka iya daukarsa tamkar mayar da martani a kan jawabin Alhaji Bafarawa a wajen kaddamar da ’yan Majalisar Yakin Neman Zabensa a Kaduna, an ruwaito Gwamna Nasir El-Rufa’i da yake neman wannan mukami a karo na biyu a inuwar jam’iyyarsu ta APC shi kuma yana mai fatan zabubbukan badin su kasance tsakanin masu gaskiya da barayi. Yana mai bayyana haduwar jiga-jigan Jam’iyyar PDP a wancan taro na Sakkwato da cewa haduwar gungun barayi ne.
Akan cikar kwarin da aka ruwaito an yi a wajen taron PDP, Gwamnan na Kaduna, ya yi zargin cewa sojojin haya ne jam’iyyar ta dauko daga kasashen makwabta, saboda wai al’ummar Jihar Sakkwato sun ki fitowa wajen taron. Ya ba da tabbacin cewa jiharsa ta Kaduna ba jihar da za ta bari PDP ta cuci jama’a ba ce. Don kuwa a fadarsa Jam’iyyar PDP, ba ta da wani abin arzikin da ta yi wa mutanen jihar ta Kaduna, don haka su ma mutanen jihar ba wani abin arziki da za su kulla da jam’iyyar ta PDP. Gwaman El-Rufa’i ya kuma nemi jama’ar jihar da a duk lokacin da za a kaddamar da gangamin neman kuri’arsa da ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, to mutanen jihar su fito kwansu da kwarkwatarsu, don su nuna wa duniya cewa ’yan asalin jihar ne suke tare da APC da gwamnatinta, ba na kasashen makwabta ba.
A fadar Gwamnan na Kaduna a cikin mulkin shekara 16 da PDP ta yi a jihar, ta tafi ta bar makarantun firamaren jihar 4,250, wasunsu ko makewayi ba su da shi, yayin da wasu rufinsu da kofofi da tagoginsu duk babu, baya ga kashi 80 zuwa 90 na yawan daliban jihar a kasa suke daukar darasi, saboda rashin kujeru da teburan zama. A nan ya bayyana ’ya’yan Jam’iyyar PDP da wadanda kawai suka kware wajen iya raba kudaden jama’a ga masu hannu da shunin junansu.
Mai karatu, bari mu fara duba kalaman Alhaji Bafarawa da yayi cewa takarar shugabancin kasar nan za ta kasance ne tsakanin mai tallar tsiya da mai tallar arziki, kuma ya kara ba da haske cewa, ya rage ga masu zabe su zabi mai arziki ko matsiyaci. Kodayake tsohon Gwamnan Sakkwaton bai ambaci suna ba, amma masu iya magana kan ce kowa ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi. Kuma zai yi wuya a ce da dan takararsu Atiku Abubakar yake yi, wanda mutanen kasa musamman wakilan da suka je zaben fitar da gwanin da zai tsaya wa Jam’iyyar PDP dan takarar Shugaban kasa da aka yi a Fatakwal babban birnin Jihar Ribas a watan Oktoban da ya gabata, Atikun ya yi nasara a kan sauran ’yan takara 12, jaridu sun bayyana cewa bayan Naira ta kare, Dalar Amurka aka rika yawo da ita ana neman canji. An kuma yi zargin cewa wanda ya fi babban tayi shi ya lashe zaben.
Idan aka bi tarihin siyasar tsohon Gwamnan Sakkwato, koda daga wannan Jamhuriyya za ka ga cewa koda tsawon shekara 8 da ya yi a gwamnan jihar daga 1999 zuwa 2007, koda wasa bai taba shiga Jam’iyyar PDP ba, karewa ma har shugaban Kwamitin Riko na Kasa baki daya ya yi wa jam’iyyarsa ta farko wato APP wadda daga bisani ta koma ANPP. Jam’iyyar da suka zauna tare da Shugaba Muhammadu Buhari, har suka ba shi takarar neman Shugabncin Kasa har karo biyu. Amma yanzu ne yake son ya fada wa ’yan kasa cewa Shugaba Buhari ya zama mai tallar tsiya, ko tun a wancan lokacin yake tallar tsiyar?
Shi kuma Gwamnan Jihar Kaduna yaushe ya bar Jam’iyyar PDP, da har zai gaya wa mutanen kasa cewa taron PDP, gungun barayi ne. Jam’iyyar da ka yi wa Minista, kodai don Allah Ya rufa maka asiri kamar sauran ’yan uwanka kuka ci tafiyar PDP na kusan dukan shekarun da ta yi tana mulki, amma daga bisani kuka zagayo kuka kewaye Shugaba Buhari, za ka ce ’yan PDP gungun barayi ne. Dukanku biyu kai da Bafarawa ba mai bakin da zai gaya wa talakan kasar nan irin maganganun da kuka fadi. ’Yan kasa da yawa sun tabbatar da cewa irinku ba wai son mulkin Buhari kuke ba, sai dai kawai don ya fi karfinku, bisa ga akidarsa ta kokarin kamanta gaskiya.
Don haka ina ganin lokaci ya yi da za ku rika gangamin yakin neman zabe na jam’iyyunku a kan ayyuka da aka yi ko ba a yi ba. Ku sa ni akasarin talakawan kasar nan ba maganganun tunzurawa suke son ji ba, maganganu me da me mai mulki ya yi a zaman cikasa alkawarin da ya yi kafin zabensa suke so.