Dan wasan gaban Dortmund, Erling Braut Haaland ya yanke shawarar barin kungiyar kuma wakilinsa ya nuna sha’awar tafiyar dan wasan zuwa Barcelona. (El Nacional)
Sai dai kuma Borussia Dortmund, na da kwarin gwiwar cewa za ta shawo kan tauraron dan wasan mai shekara, 21 wanda Manchester City da Chelsea ke zawarci ya ci gaba da zama, duk da cewa akwai damar sayensa ga duk kungiyar da ta biya fam miliyan 64 na na-gani-ina-so, kamar yadda yarjejeniyarsa da kungiyar ta Jamus ta tanada, damar da za ta samu a shekara mai zuwa. (Manchester Evening News)
Watakila dan wasan gaban Paris St-Germain, Kylian Mbappe ya bukaci a saka batun gasar Olympics a duk wata yarjejeniya da zai saka wa hannu da Real Madrid bayan dan wasan mai shekara 22 ya fito fili ya bayyana aniyarsa ta wakiltar Faransa a wasan Olympics da za a buga a Paris a 2024.
Antonio Conte na shirin sa dan wasan tsakiya na AC Milann dan Ivory Coast Franck Kessie mai shekara 24 zama dan wasansa na farko da zai saya a matsayin sabon kociyar Tottenham. (Metro)
Haka kuma Conte yana son Tottenham ta sayo dan bayan Inter Milan, dan Holland, Stefan de Vrij, mai shekara 29, a watan Janairu. (Football Insider)
Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid Eden Hazard ya tafi Newcastle a lokacin kasuwar ’yan kwallo ta watan Janairun, kuma kociyan kungiyar ta La Liga Carlo Ancelotti a shirye yake ya bar shi ya tafi. (Star)
Ana sa ran Newcastle za ta nemi tsohon dan wasan tsakiyan Liverpool Philippe Coutinho inda ake ganin Barcelona ta kagara ta rabu da dan wasan na Brazil mai shekara 29. (Sport)
Manchester United na shirin fara neman dan wasan tsakiyan Monaco kuma dan kasar Faransa Aurelien Tchouameni mai shekara 21 a yayin da suke neman wanda zai maye gurbin dan wasan Faransar nan mai shekara 28 Paul Pogba. (Football)
Shi dai Paul Pogba a yanzu ya fi son ya koma inda ya fito Juventus a kan ya je Paris St-Germain ko Real Madrid a karshen zamansa da Manchester United, a kaka mai zuwa lokacin da dan wasan na tsakiya mai shekara 28 zai kasance ba shi da wani kwantiragi a kansa. (Gazzetta dello Sport )
Kocin Villarreal Unai Emery mai shekara 50 ya fasa komawa Newcastle sakamakon kulob din na so ya saka wani sakin layi a kwantiraginsa da zai ba Newcastle din damar korarsa muddin ta zama kashin baya karshen kaka. (Daily Mirror)
Manchester City ta shaida wa kocin Leicester Brendan Rodgers mai shekara 48 cewa za ta bukace shi idan Pep Guardiola mai shekara 50 ya bar kulob din. (The Transfer Podcast via Leicester Mercury)
Barcelona na sa ran zaunar da Ousmane Dembele mai shekara 24 domin dan wasan na Faransa ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ta shekara uku a karshen Nuwamba.
Dembele wanda kwantiraginsa zai kare a kaka mai zuwa , ana rade-radin cewa ya amince da rage masa albashi. (Mundo Deportivo – in Spanish)
Barcelona za ta shiga zawarcin dan wasan tsakiyan Tottenham mai shekara 24, Tangu Ndombele a watan Janairu, sai dai aro kawai ake ganin za ta iya daukar dan wasan na Faransa. (Sport – in Spanish)