✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gyaran Magudanar Soyayya

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo…

Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau insha Allah za mu yi bayani kan hanyoyin da ma’aurata za su bi don gyara magudanar soyayyar auratayyarsu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Yanayin Soyayya
Da farko, yana da kyau ma’aurata su fahimci cewa soyayya ita ce babban makasudin kasancewarsu ma’auratan juna, ita ce muhallin auratayya; in ba soyayya a cikin rayuwar aure, to auren nan zai zama fanko ba rahma a cikinsa; haka kuma soyayya ita ce dadin auratayya, auren da ba soyayya a cikinsa za ka same shi lami ba dandano a cikinsa, ko kuma a samu dandanonsa me daci ko hamami.
Soyayya kuwa kalma ce ta aiki mai gudana wadda ake cikin yin ta a kodayaushe ba dakatawa; haka ma manyan sinadaran da suka gina soyayya; kaunatayya da kulawa dukkansu aikatau ne masu gudana. Al’amura da dama na faruwa cikin rayuwar aure, wadanda a hankali suna taruwa har su yi yawa su lullude soyayya kuma su cushe magudanarta, sai ta tsaya cak ba ta gudana; duk soyayyar da ba ta gudana kuwa to kamar babu ita ne, domin ma’aurata ba su amfana da ita. Don haka sai ma’aurata su bi wadannan hanyoyin don gano matsalolin da suka taushe soyayyarsu har ya zamana ba ta gudana.
1.    Bincike
Ba a iya maganin matsala har sai an gano yanayinta da abin da ke haifar da ita; don samun saukin gyara magudanar soyayya, sai ma’auarata su binciki kansu game da soyayyarsu kuma su yi kyakkyawan nazari kan wasu al’amura da suka shafi soyayyarsu da kuma gano hanyoyin magance wadannan matsalolin.
Ga wasu jerin tambayoyi da ma’aurata za su amsa don gane inda soyayyarsu ke da tangarda da kuma abin da ya haifar da wannan tangardar:
1.    Ina son Mijina/Matata kuwa?
2.    Me Ya sa nake son shi/ta?
3.    Yaushe na fara son shi/ta?
4.    Shin son yana karuwa ne ko raguwa?
5.    Me ya sa shi karuwa/raguwa?
6.    Akwai wani laifi da ya sa na rage son shi/ta?
7.    Ina ganin kima da darajarsa/ta kuwa?
8.    Akwai wani laifi da ya yi/ta yi min da ya sa ba na ganin kimarsa/ta kamar da?
9.    In na gan shi/ta ya nake ji, dadi da murna; bakinciki da haushi; ko bani jin komi?
10.    Ina bayyanar da soyayya ta gare shi/ta kuwa: In amsar ‘I’ ne; ta wadanne irin hanyoyi ne; in kuma a’a, me ya sa?
11.    Shin mijina/matata na sona kuwa?
12.    Ta wadanne hanyoyi nake gane yana/tana sona?
13.    In kuwa ba ya sona/ba ta sona, me ya sa?
14.    Yaushe nake jin ya/ta daina sona?
15.    Wani laifi na yi da ya sa ya/ta daina sona?
16.    Ya zan ji yau a wayi gari a ce mijina/matata ba ya/ba ta duniya?
Ma’aurata na iya kara wasu tambayoyin da suka dace da yanayinsu.
2.    Gyaran Fuska
Amsa wadancan tambayoyi da ke sama zai ba ma’aurata hoton irin yanayin da soyayyarsu take, zai sa su fahimci matsalolin da suka cushe magudanar soyayyarsu; don haka sai su sami takarda su rubuta dukkan inda suke ganin akwai wata matsala, su binciko abin da ke haifar da wannan matsala sannan su yi nazarin hanyar da suke ganin zai kawar masu da wannan matsala; in matsalar daya daga cikinsu ke haifar da ita, sai ya yi aniyar yin dukkan kokari don ganin ya kawar da wannan matsala; in kuwa dukansu ne ke da hannu cikin matsalar, sai su yi dukkan kokarin magance wannan matsala.
3.    Hadaka Soyayya
Bayan ma’aurata sun gano matsalolin da suka cushe magudanar soyayyarsu kuma sun magance wannan matsala, daga nan sai su yi kokarin yin abubuwan da za su hadaka soyayyarsu; ta kara yawa da inganci. Ta hanyar gano sababbin hanyoyin dadadawa da faranta wa juna rai; ta hanyar yin kokarin kara yawan lokacin kasancewa tare ba wai dole sai lokacin barci kadai ba; ta hanyar yin sabon dashen kauna cikin zuciyar juna; ta hanyar yawan sabunta kaunatayyarsu da soyayyarsu a-kai-a-kai; ta hanyar cakuda so da kauna da romansiyya cikin ibadar aurensu; da duk wasu hanyoyin da suke ganin za su hadaka tare da kara rayar da soyayyarsu cikin zuciyar juna; insha Allah bayani na zuwa kan kyawawan hanyoyin da ma’aurata za su bi wajen bayyanar da soyayya ga junansu.
Ma’aurata sai a mike tsaye, a kuma dage a yi dukkan kokarin da ya kamata don yin gyara ga muhallin auratayya; kar a yi ta zaman hakuri ana rayuwar auratayya kamar ba soyayya; duk wani abu da ke hana bayyanar da soyayyar ga juna ya kamata a yi fatali da shi domin ba amfanin da yake ga rayauwar aurensu, kuma ko da yana yi din, tabbas bayyanar da soyayyar ga juna tafi zama alfanu. Ku tuna, rayukanmu duka ba a hannunmu suke ba, ba wanda ya san ranar mutuwarsa, mutuwa na iya dauke abokin aurenku, sannan ne za ku rika da na sani na yi masa kaza ko na ce mata kaza? Da fatan Allah, wanda zuciyoyin dukkan mai rai ke karkashin ikonSa, wanda ke shamakancewa tsakanin mutum da zuciyarsa, ya cika zuciyar dukkanin ma’aurata da so, kauna, kulawa da sha’awar juna, amin.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.