A ranar Litinin da ta wuce ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen kasar Fotugal Cristiano Ronaldo ya lashe gasar Gwarzon dan kwallon Duniya da aka fi sani da Ballon D’or da Hukumar shirya kwallon kafa ta duniya FIFA ta ke gudanarwa a duk shekara, a karo na biyu.
Ronaldo ya doke abokan takarsa ne watau Lionel Messi, dan kwallon FC Barcelona da ke Sifen da Frank Ribery, dan kwallon Bayern Munich da ke Jamus.
Sai dai abin da ya fi jan hankalin ’yan kallo shi ne yadda dan kwallon ya rika zubar da hayewa jim kadan bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe gasar.
Masana harkar kwallo sun ce watakila Ronaldo ya zubar da hawaye ne saboda murnar lashe kyautar a karo na biyu tun bayan da ya lashe a shekarar 2008 a lokacin da yake buga wa kulob din Manchester United da ke Ingila kwallo. Wasu kuwa sun ce watakila dan kwallon ya yi kuka ne ganin yadda ya sha wahala kafin ya sake lashe kyautar musamman yadda ya rika gwagwarmaya da Lionel Messi a kusan shekaru da dama amma sai a wannan lokaci ya samu nasarar lashe ta a karo na biyu.
A lokacin da Ronaldo yake zubar da hawaye, shi ma shaharsarren dan kwallon duniya Pele dan asalin Brazil ya rika zubar da hayawe don tausaya wa dan kwallon.
Ronaldo dai ya halarci wurin bikin ne da aka gudanar a Hedkwatar Hukumar FIFA da ke Zurich a kasar Swazilan tare da dansa da budurwarsa da kuma mahaifiyarsa don su taya shi murna.
Jim kadan da karbar kyautar ce sai ya yi bayanai masu sosa rai inda ya godewa abokan kwallonsa na kulob din Real Madrid da abokan wasansa na kasar Fotugal da ’yan uwa da abokan arziki da kuma magoya bayansa da ke daukacin duniya musamman wadanda suka tallafa masa wajen kai wa ga samun nasarar lashe kyautar.
Kafin wannan lokaci, Lionel Messi ne ya kafa tarihin lashe kyautar sau hudu a jere. Shi kuwa abokin takara na uku watau Frank Ribery bai taba lashe ta ba, kuma masana harkar kwallo suna ganin da wuya dan kwallon ya sake samun dama irin wannan tun da bai samu nasarar lashe kyautar a wannan karo ba.
Masu horarwa na kungiyoyin kwallon kafa daga sassan duniya da kyaftin-kyaftin da kuma ’yan jaridu wadanda Hukumar FIFA ta zabo ne suka gudanar da zaben.
Haka kuma an zabi tsohon Kocin kulob din Bayern Munich Jepp Heynckes a matsayin Gwarzon mai horarwa na shekarar 2013 yayin da aka zabi shahararren dan kwallon duniya Pele Gwarzon dan kwallon Duniya na karni watau (World Football Player of the Century).
Gwarzon dan kwallon Duniya: Ronaldo ya zubar da hawaye
A ranar Litinin da ta wuce ne shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid da ke Sifen kuma haifaffen kasar Fotugal Cristiano Ronaldo ya lashe…
