✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnonin PDP sun goyi bayan hana kiwon-sake

Gwamnonin sun ce kiwon zamani shi ne zai magance rikicin manoma da makiyaya.

Zauren gwamnoni karkashin inuwar Jam’iyyar PDP sun yi ittifaki kan haramta kiwon-sake a zaman abin da zai magance rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.

Gwamnonin yayin taron da suka yi a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo a ranar Litinin sun jaddada cewa tsarin kiwon killace dabbobi na zamani shi ne kawai mafita ga matsalar rikicin manoma da makiyaya a kasar.

Sun kuma tattauna kan halin rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arzikin da Najeriya ke fama da shi.

Gwamnoni da suka halarci taron sun hada da: Nyesom Ezenwo Wike na Jihar Ribas, Udom Emmanuel na Akwa Ibom, Douye Diri na Bayelsa, Samuel Ortom na Benuwai; sai Ifeanyi Ugwuanyi, Gwamnan Jihar Enugu.

Sauran su ne Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta, Ahmadu Umaru Fintini na Adamawa, Godwin Obaseki na Edo, Bala Mohammed na Jihar Bauchi da Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Mohammed.