✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

2023: Dalilin da gwamnonin Arewa ke son Jonathan ya dawo

Dalilan da gwamnonin Arewa ke son Jonathan ya zama shugaban kasa a 2023.

A baya-bayan nan sunan tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan, ya tayar da kura a fagen siyasar kasar, musamman kan batun zaben 2023.

Daily Trust ta ruwaito wani tsohon gwamna yana cewa wasu gwamnonin jam’iyyar APC biyu ne suke jagorantar tafiyar Jonathan din, kuma sun tallata shi ga Fadar Shugaban Kasa.

“Su (an sakaya sunayensu) ne suke tallata tafiyar Jonathan domin su taka wa Bola Tinubu burki, bayan sun lura cewa mataimakin shugaban kasa ba shi da karfin karawa da Tinubu,” inji tsohon gwamnan.

Mutane da dama dai sun saki baki da jin cewa an saya wa tsohon shugaban kasar fom din takarar komawa kan kujerar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC.

Amma bayan kurar da batun ya tayar, Jonathan ya fito ta hannun kakakinsa, Ikechukwu Eze, ya ce ba da yawunsa aka sayi fom din ba, sannan ya nesanta kansa da takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Majiyoyinmu sun shaida mana cewa wasu gwamnoni masu ci daga yankin Arewa, kuma na hannun daman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne suka saya wa Jonathan fom din.

Wakilinmu ya tambayi tsohon gwamnan dalilin da ’yan APC ke son tsohon shugaban kasar, inda ya kada baki ya ce, “Suna da nasu manufar; mutumin da wa’adin mulki daya kawai zai yi suke so, kuma suna so ya dauke su a matsayin mataimakin shugaban kasa”.

Buhari ne kan gaba

Duk da cewa rsohon gwamnan, wanda shi ma na hannun daman Shugaban Buhari ne, ya ce gwamnonin biyu sun dauko maganar Jonathan ne “domin biyan bukatun kansu,’’ amma wata majiyar tamu ta ce Shugaba Buhari ne ke son dawowar Jonathan.

“Babban magoyin bayansa shi ne Shugaban Kasa, kana ganin zai fara tunanin yin hakan in ba tare da ya samu goyon bayan ‘Baba’ ba?

“Bai fito fili ya fada ba cewa yana so; Ana son ya fito ne saboda an fi nutsuwa da shi ya zama magajin Buhari,” inji shi.

Jonathan zai koma APC

A watan Afrilu ne tsohon Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar APC Reshen Jihar Bayelsa, Diekivie Ikiogha, ya ce saura kiris tsohon shugaban kasar ya fice daga PDP.

“Zai bayyana ne bisa gayyatar da APC ta yi mishi na ya fito, kuma yana nazari a kai; an riga an gama abubuwa da yawa, ana ci gaba da tattauanwa kuma za a gayyace shi.

“Muna kokarin shawo kansa kuma ina ganin zai amsa kiran, idan komai ya daidaita kuma zai tsaya takara,” a cewarsa.

Yana da ’yancin fitowa

Wani mai sharhi kan al’amura, David West, ya ce duk da cewa a baya tsohon shugaban ya sanar cewa ya daina siyasar jam’iyya, yana da ’yancin tsayawa takarar kowace kujera a Najeriya. 

Amma ya ce da wuya Jonathan ya tabuka wani abu fiye da yadda aka gani a lokacin mulkinsa na farko.

“Na san idan aka ba shi mulkin Najeriya, shekara hudu rak zai yi, akasin hakan kuma zai haifar da da rikici.” 

Dalilin saya wa Jonathan fom?

“Majiyoyi da dama masu kusanci da lamarin sun bayyana cewa gwamnonin biyu, wadanda na hannun daman Shugaba Buhari ne, sun ja ra’ayin wani bangare na Fadar Shugaban Kasa domin cim ma manufarsu ta shigar tsohon shugaban kasar takarar shugaban kasa.

“Majiyoyin sun kuma bayyana wa wakilanmu sunan gwamnonin da ke wannan yunkuri, amma muka ba mu bayyana su ba, kasancewar ba mu samu jin ta bakinsu ba zuwa lokacin hada wannan rahoton, sun yi tafiya kasar waje.

“Daya gwamna ya fito ne daga Arewa maso Yamma, dayan kuma daga Arewa maso Gabas, kuma tun shekarar da ta gabata suka fara wannan yunkuri, amma daga baya suka jingine shi domin tallata takarar Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

“Amma da gwamnonin suka ga takarar Emefiele ba ta samu karbuwa sosai ba, sai suka koma kan shirinsu na Jonathan.

“Gwamnonin suna taka muhimmiyar rawa a jam’iyyar APC a cikin ’yan shekarun nan.

“Shi kansa Jonathan daga take-takensa ya nuna yana ra’ayin hakan,” inji rahoton na  Daily Trust.

Ku jira ku gani, inji Jonathan

Idan ba a manta ba, baya tsohon shguaban ya ce wa masu kiraye-kirayen ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 cewa, “Ku jira ku gani.”

Hakan ta sa ake ganin yana nazari ne kafin ya bayyana ra’ayinsa da kuma jam’iyyar da zai fito takarar a inuwarta.

A babban zaben 2015 ne dai Shugaba Jonathan na jam’iyyar PDP, a lokacin, ya sha kaye a hannun  dan takarar jam’iyyar adawa ta APC, Muhammadu Buhari, wanda ya kawo karshen shekara 16 da PDP ta yi a jere tana mulkin Najeriya, tun daga 1999.

Sai dai a tsawon shekara shida da suka gabata, ba a ganin shi a tarukan PDP.

A hannu guda kuma alakarsa da Shugaba Buhari da manyan kusoshin jam’iyyar APC na kara karfi, lamarin da wasu kusoshin jam’iyyar adawar ba su yi na’am da shi ba.

Jonathan ba dan APC ba ne

Amma Shugaban Jam’iyyar APC Reshen Jihar Bayelsa, mahaifar Jonahta, Dokta Dennis Otiotio, ya ce har yanzu tsohon shugaban kasa bai shiga jam’iyyar ba.

Amma ya bayyana cewa duk da haka Jonathan din na da ’yancin shigar ta a duk lokacin da ya ga dama.

Dennis ya bayyana hakan ne a ranar Talata kan yunkurin masu son ganin tsohon shugaban kasar ya fito takara a APC a zaben 2023.

Ya ce, “Har yaznu tsohon shugaban kasar bai yi rajista da APC ba, amma yana da ’yancin yin haka, kuma shirye muke mu karbe shi.

“A matsayinmu na jam’iyya, babban burinmu shi ne mu lashe zabe, kuma hanyar da za mu iya yin hakan cikin sauki kawai ita ce ta karbar karin mutane a cikinmu,” inji Dokta Dennis.