✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Zamfara za ta gina katanga a makarantu 40 don kare ɗalibai

Kwamishinan ya ce gwamnatin za ta yi aikin ke domin inganta tsaro da bunƙasa ilimi.

Gwamnatin Jihar Zamfara, ta bayyana cewa za ta zagaye makarantu 40 na sakandare da katanga domin inganta tsaro da kare kayayyakin gwamnati.

Kwamishinan Ilimin Kimiyya da Fasaha na jihar, Malam Wadatau Madawaki, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da wata ƙungiya a ma’aikatarsa a ranar Asabar.

Ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na tabbatar da tsaro da kuma inganta harkar ilimi a jihar.

Ya ce gina katanga a makarantu zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da natsuwa a tsakanin ɗalibai da malaman makaranta.

Haka kuma, zai rage yawan matsalolin tsaro da ake fuskanta a kusa da makarantun.

Malam Wadatau, ya ƙara da cewa an fara da makarantun 40 ne da aka fi ganin suna da buƙatar kulawar gaggawa, duba da yankin da suke.

Ya ce za a ci gaba da faɗaɗa aikin har zuwa sauran makarantun a faɗin jihar.

Kwamishinan ya buƙaci haɗin kai daga shugabannin al’umma da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar wannan aiki.

“Muna roƙon kowa ya mara wa gwamnati baya domin tabbatar da tsaron makarantu da ci gaban ilimi a Jihar Zamfara,” in ji shi.