✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin yada labarai 4 saboda yada taron PDP

Kafofin Yada Labaran sun saba wa ka'idar aikinsu da umarnin gwamnati.

Gwamnatin Zamfara ta rufe wasu gidajen rediyo da talabijin 4 da ke jihar saboda yada taron gangami da jama’iyyar PDP ta gudanar a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan ta gidan rediyon jihar a ranar Lahadi.

Kafofin yada labaran da rufewar ta shafa sun hada da tashar radio ta Pride FM da Vision FM da gidan Talabijin na NTA da Gamji TV da al’umma TV.

Kwamashinan ya bayyana cewa an rufe su ne saboda sun saba wa ka’idar aikinsu ta hanyar yada taron jam’iyyar adawa ta PDP duk da cewa gwamnatin jihar ta haramta tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro.

“Gwamnati ta dakatar duk wani taron siyasa a jihar saboda matsalar tsaro, amma jam’iyyar PDP ta yi watsi da wannan hani, ta yi taron ta, a inda aka kashe mutum daya, 18 kuma suka jikkata,” in ji Dosara.

Kwamishinan ya kuma ce, gwamnati ta umarci jami’an tsaro da su kama duka wani ma’aikacin kafofin yada labaran da aka rufe da ya kuskura ya je ofis da sunan aiki.

Wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin shugabannin kafar yada labaran da aka rufe, amma ya ce shi ba zai ce komai ba.

Sai dai ya ce shugaban kungiyar su ta kafofin yada labarai masu zaman kan su zai sanar da matsayarsu bayan taron da za su yi ranar Lahadi.