✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Zamfara ta haramta tarukan siyasa saboda tsaro

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin domin tabbatar da tsaro a jihar.

Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari.

Dalilin Haramta Tarukan Siyasa

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru.

Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk wani taro ko gangami da zai iya haddasa tashin hankali, musamman ganin yadda aka rasa rayuka da ƙone dukiya mai yawa a Ƙaramar Hukumar.”

Ya kuma ƙara da cewa wannan dakatarwa ba ta dindindin ba ce, illa dai mataki ne na wucin gadi domin kiyaye zaman lafiya a jihar.

Martanin Jam’iyyar APC

A nata ɓangaren, jam’iyyar APC reshen Zamfara, ta soki matakin, inda ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda tsoron ƙarfin jam’iyyar a jihar.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Malam Yusuf Idris Gusau, ya ce: “Ai abin mamaki ne a ce an hana tarukan siyasa, domin ba gangamin yaƙin neman zaɓe aka shirya ba.

“Babu wata doka da ta hana tarukan jam’iyyu, don haka gwamnati ba ta da hurumin hana mu gudanar da harkokinmu na siyasa.”

Ya ƙara da cewa APC jam’iyya ce mai rijista a ƙasa, kuma mabiyanta suna bin doka ba tare da haddasa wata fitina ba.

Fargabar Ƙarin Tashin Hankali

Ana dai ganin wannan mataki na gwamnati da martanin APC na iya ƙara dagula lamarin siyasa a jihar.

Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai buƙatar a samu tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, tare da shiga tsakani da dattawa da jami’an tsaro domin hana rikicin ya tsananta.