✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Tinubu na shirin kama ni — Hadimin Atiku

Hadimin ta ce yana da sahihan bayanan da suke nuna ana shirin tsare shi.

Daniel Bwala, mai taimaka wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shirya makarkashiyar kama shi tare da tsare shi.

Lauyan ya yi wannan zargin ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter), aranar Litinin.

Ya yi ikirarin cewa yana da wasu sahihan bayanai daga wasu mutane a fadar shugaban kasa na shirin yin amfani da jami’an tsaro wajen kama shi tare da tsare shi.

Bwala ya wallafa: “A daren jiya na samu sahihin bayanan sirri cewa wasu manyan mutane da ke Villa na wannan gwamnati na shirin yin amfani da jami’an tsaro su kama ni tare da kai ni gidan yari.

“Bari duniya ta sani a yau cewa a ko yaushe na san cewa daga matsayina na adawar siyasa. Idan wani abu ya same ni, bari duniya ta san mugun shirinsu a yau.”

Aminiya ta ruwaito cewa Bwala na daya daga cikin wadanda suka fice daga jam’iyyar APC bayan da jam’iyyar ta fitar da ‘yan takararta shugaban kasa a zaben 2023.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels, ya bayyana cewar zabar Kashim Shettima da Tinubu ya yi, ba alheri ne ga jam’iyyar APC ba.