Ministan Sufurin Jiragen Sama a Najeriya, Sanata Hadi Sirika, ya ce za a bude reshen zirga-zirgar jiragen saman kasa-da-kasa na filin jirgin saman Malam Aminu Kano daga ranar 5 ga watan Afrilun 2021.
A ranar Litinin ce Ministan ya bayyana hakan yayin taron kwamitin kar ta kwana na shugaban kasa kan yaki da cutar Coronavirus wanda aka gudanar a birnin Abuja.
- Dalilin haramta sinadaran karin dandano a Kano
- An ceto mata hudu masu juna biyu a gidan sayar da jarirai
- Abin da ya sa ake sace dalibai a makarantu a Arewa
Ya kuma ce za a bude filayen jirgin saman Fatakwal da Enugu domin dawo da jigilar kasa-da-kasa a ranar 15 ga watan Afrilu da kuma 3 ga watan Mayu na bana.
“A cewarsa, “an rufe filayen jirgin saman ne kamar yadda aka rufe na sauran kasashe a fadin duniya kuma mun rufe na kasarmu ne saboda ta nan ne kwayoyin wannan cutar ta Coronavirus ta shigo mana.”
“Mun bude wasu daga cikinsu bayan la’akari da shawararin da muka samu a wajen masu ruwa da tsaki kuma babu wasu dalilai na kashin kai da suka hana a sake bude filin jirgin saman Kano da na wasu jihohin saboda akwai matakai da aka tanada,” in ji Ministan.
Tun bayan bullar cutar Coronavirus da ta sanya aka haramta zirga-zirga a ciki da wajen kasashe, Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe kafatanin filayen jirgin saman kasar a wani yunkuri na takaita yaduwar cutar.
Daga bisani gwamnatin ta bude filayen jirgin saman Legas da na Abuja inda aka ci gaba da jigilar kasa-da-kasa.
Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta sake bude reshen jigilar kasa-da-kasa na filin jirgin saman Malam Aminu Kano bayan shafe tsawon watanni a rufe.