✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gwamnatin Tarayya ta haramta sayar da naman daji a Najeriya

Mafarauta da dillalan naman daji dole ne su daina wannan al’adar.

Gwamnatin Tarayya ta sanar da haramta sayarwa da cin naman daji a wani yunkuri na dakile yaduwar cutar kyandar birrai a Najeriya.

Ministan Noma da Raya Karkara, Dokta Mohammad Abubakar ya umurci mafarauta da dillalan naman daji a kasar da su daina sana’ar.

Naman Daji da aka haramta ci ko sayarwa sun hada da duk wani dabbar daji da aka kashe don cinyewa, kama daga tururuwa, birin daji, jemagu na ’ya’yan itace, bera, da macizai.

Abubakar ya kuma bukaci ’yan Najeriya su guji cudanya da mutanen da ake zargin suna dauke da cutar kyandar biri.

A cewarsa, dole ne a dakatar da jigilar shigowa da dabbobin daji a cikin gida da kuma kan iyakokin kasar

“Mafarauta da dillalan ‘naman daji’ dole ne su daina wannan al’adar don hana duk wata yiwuwar ‘zubewa’ na kwayar cutar a Najeriya.

Abubakar ya kuma kara da cewa, ma’aikatar tana hada kai da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) da sauran masu ruwa da tsaki a cikin tawagar lafiya daya domin ganin an shawo kan lamarin tare da takaita shi.

A farkon makon nan ne Najeriya ta tabbatar da bullar cutar kyandar biri har guda 21 tun daga farkon shekarar 2022, inda aka samu rahoton mutuwar mutum guda, in ji Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Najeriya (NCDC).

Kyandar biri, cutar da kwayoyinta ba su da karfi, na yaduwa a Najeriya a yankunan kauye, musamman inda suke da matsanancin zafi.