Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Kasa (NDCD) ta ce, ya zuwa 23 ga Disamba mutum 49 ne aka tabbatar sun kamu da cutar Kyandar Biri a fadin Najeriya.
NCDC ta bayyana hakan ne ta shafinta na intanet a ranar Alhamis.
- Hana mata aikin jinkai ta haifar wa MDD tsaiko a Afghanistan
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Tabbatar Da Zaman Lafiya A Harkokin Zabe
Ta ce kasar na fuskantar karuwar masu kamuwa da cuta, duk da cewa tana bakin kokarinta wajen yaki da yaduwarta.
Kamfanin Dilancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na cewa tana taimaka wa kasar gwargwadon hali wajen yaki da cutar.
Tun a 2017 aka samu bullar cutar a Najeriya, inda gwamnati ke ci gaba da kokarin ganin ta dakile yaduwarta.
Rahotanni sun ce ya zuwa 23 ga Disamba, 2022 mutum 83,483 aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya, 275 sun mutu a tsakanin kasashe 110.
(NAN)