✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta ba wa al'ummar yankin Samaru da ke Karamar Hukumar Zariya gudummawar cibiyar kula da lafiya a matakin farko

Rundunar Sojian Ruwa ta Najeriya jaddada kudurinta na bunkasa dangantakarta da fararen hula don kara samun goyon bayan da al’umma ga ayyukan sojojin.

Babban Hafsan rundunar, Vice Admiral Emmanuel Ogalla ya bayyana haka lokacin bukin kaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko da rundunar ta bai wa al’ummar Samaru gudunmuwa a Zariya.

Ya yi bayanin cewa samar da cibiyar kulana daga cikin shirin da rundunar ta bullo dashi domin karrama Rear Admiral Ibrahim Dewu.

Babban hafsan sojan ruwan, wanda Rear Admiral J.A. Nwagu ya wakilta , ya ce, an bullo da shirin ne domin inganta rayuwar al’ummomin da duk mai mukamin Rear Admiral ya fito cikinsu.

A jawabinsa, Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, wanda Babban Daraktan Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko, Dakta Bello Jamoh ya wakilta ya ce, samar da cibiyar zai kawo karin bunkasar kiwon lafiya ga yankin Samaru da kewaye.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa inganta rayuwar al’umma fifiko, musamman a bangaren kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara da hana yaduwar cututtuka da kuma rigakafi.

Da yake jawabi tunda farko, Mai Martaba Sarkin zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli ya roki rundunar sojan ruwan da ta kammala aikin makarantar sakandaren da ta fara a Farakwai da ke yankin Karamar Hukumar Igabi.

Ya ce farfado da makarantar zai kara dankon dangantakar da ke tsakanin sojoji da farar hula da samar da karin tsaro da cigaba a yankin.

Sarkin, wanda hakimin Basawa, Alhaji Haruna Bamalli ya wakilce shi ya kuma roki al’ummar Samaru da su yi amfani da asibitin yadda ya dace, ya kuma yaba wa Rear Admiral Ibrahim Dewu bisa kokarin da ya yi wajen samar wa al’ummar Samaru wannan asibitin.