Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da yaƙi da kawar da cutar shan-inna ta 2024 a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu da ke Jihar.
Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta bayar da cikakken goyon baya wajen yaƙar cutar shan-inna da sauran cututtukan da suke addabar ƙananan yara.
- EFCC ta kai samame Jami’ar Dan Fodio, ta yi awon gaba da ɗalibai
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana hutun Ranar Samun ‘Yanci Kai a Nijeriya
Mai magana da yawun Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa akwai buƙatar yi wa dukkanin ƙananan yara da suka dace rigakafin cutar.
A cewarsa hakan zai kar6a musu kariya da ƙarfafa garkuwar jikinsu, tare da daƙile yaɗuwar cutar, musamman ganin cewa Kano tana daga cikin jihohi 18 da ke cikin hatsarin yaɗuwar cutar a Najeriya.
A jawabinsa, Gwamna Yusuf, ya jaddada muhimmancin ƙara kaimi wajen yi wa yara rigakafi.
Ya ce gwamnatinsa za ta haɗa kai da hukumomin lafiya da al’ummomi don tabbatar da rigakafin ya isa ko ina a faɗin Kano.
Duk da cewa Najeriya ta samu takardar shaidar kawar da cutar shan-inna a watan Agustan 2020, gwamnan ya ce Kano ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba, za ta tabbatar ana yi wa yara allurar rigakafi akai-akai.
“Za mu ci gaba da sanya ido da kuma tabbatar da ana yi wa yara rigakafi a kai a kai don kare su,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su yi amfani da wannan dama don yi wa ’ya’yansu rigakafi tare da kula da tsafta da tsare-tsaren lafiya don amfanin al’umma baki ɗaya.
Gwamna Yusuf, ya gode wa ƙungiyoyi, shugabannin addinai da masarautun jihar bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnatisa.
Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen lafiya don inganta rayuwar al’ummar Kano.
Mataimakin Gwamnan jihar, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ke jagorantar kwamitin yaƙi da cutar shan-inna a jihar, ya yaba wa jajircewar gwamnan kan inganta harkar kiwon lafiya.
Ya ce, “Tafiyar gwamna da jajircewarsa abin a yaba ne.”
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana cewa an zaɓi Dawakin Kudu domin kaddamar da yaƙin ne saboda tana fuskantar ƙalubalen kiwon lafiya.
A cewarsa ƙaramar hukumar na fuskantar ƙarancin allurar rigakafi.
Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, wanda Dakta Bashir Muhammad Dankadai ya wakilta, ya jaddada buƙatar wayar da kan jama’a yadda ya kamata.
Ya yi kira ga magidanta da su rungumi yin rigakafi akai-akai domin kare yara.
Yaƙin kawar da cutar shan-inna na 2024 wani ɓangare ne, na ci gaba da ƙoƙarin Jihar Kano wajen kare lafiyar ƙananan yara da tabbatar da Najeriya ta ci gaba da kasancewa ba ta da cutar shan-inna.