Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta kasa (NCDC), ta ce mutane 170 ne suka rasu daga farkon shekarar nan zuwa yanzu sakamakon zazzabin Lassa.
A wani rahoton da hukumar ta wallafa, ta ce ta damu matuka kan yadda cutar ke kara yaduwa a kasar, domin yanzu haka mutane 909 ta tabbatar sun kamu, daga cikin 6,547 da ake zargin na dauke da ita.
- Yadda rasuwar Sarauniya Ingila ta kawo wa ’yan kasuwa ciniki
- Mutum 700,000 ke kashe kansu a duk shekara —WHO
Haka kuma ta ce daga makon farko zuwa na 35 na shekarar 2022, an samu mutuwar mutane 170.
Sai dai ya ce an samu raguwar mace-macen masu dauke da cutar da kashi 18.7, idan aka kwatanta da na 2021 da aka samu kashi 22.7.
“Sai dai kuma adadin wadanda ake zargin suna dauke da ita ya karu idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
“Jimillar jihohi 25 ne ke da masu dauke da cutar da suka fito daga kananan hukumomi 101 a shekarar 2022.
“Daga cikin wadanda aka gwada aka ga suna dauke da ita kuma, kaso 70 sun fito ne daga Jihar Ondo, da Edo da kuma Bauchi”, a cewar rahoton.
Rahoton ya kuma ci gaba da cewa, tun daga ranar 29 ga watan Agusta zuwa 4 ga watan Satumba, adadin wadanda aka yi wa gwaji aka tabbatar suna dauke da Lassan ya karu zuwa mutane 10.
Haka kuma NCDCn ta ce har a mako na 35 na shekarar ta 2022, babu wani sabon ma’aikacin lafiya da aka samu ya kamu da ita.
A wani rahoton mai nasaba da wannan da NCDC ta fitar a ranar Lahadi, an samu jimillar mutane 36 da suka kamu da cutar kyandar biri a jihohi 14 cikin mako guda.
Daga cikin wannan adadin ta ce an samu mutuwar mutane shida daga jihohin Delta da Legas da Ondo da Akwa Ibom da Kogi da kuma Taraba.
Ta ce, daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 28 ga watan Agusta, Najeriya ta samu mutane 704 da ake zargin sun kamu da ita, yayin da 277 aka tabbatar da suna dauke da ita.
Haka zalika, ta ce daga cikin adadin, maza 186 ne masu ita, sai mata 91 da suka fito daga jihohi 30.