Gwamnatin Jihar Abiya ta tabbatar cewa mutum tara sun kamu da cutar Kyandar Biri a fadin jihar.
Babbar Jami’ar Lafiya ta jihar, Misis Peace Nwogwugwu ce ta bayyana hakan a Umuahia babban birnin jihar a ranar Laraba.
- Matar mai wakar ‘Najeriya Jaga-Jaga’ ta ba da kodarta an dasa masa
- NAJERIYA A YAU: Zaben 2023: Shin Zai Yiwu A Tura Sakamako Ta Intanet?
Ta ba da tabbacin ne sa’ilin da take jawabi a wajen taron kara wa juna ilimi na yini daya da Kungiyar Mata ’Yan Jarida ta Najeriya (NAWOJ) tare da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Abiya suka shirya.
Ta ce, “A halin da ake ciki, an gudanar da bincike a kan mutum 40 da ake zargin sun kamu da Kyandar Biri, inda aka tabbatar da mutum tara daga kananan hukumomi biyar a jihar na dauke da cutar.”
Ta kara da cewa, kananan hukumomin da lamarin ya shafa sun hada da, “Umuahia ta Arewa da Umuahia ta Kudu da Ikwuano da kuma Umunneochi wadanda kowacce ke da mutum biyu-biyu da suka kamu da cutar, sai kuma karamar hukumar Aba ta Arewa da ke da mutum daya.”
“Gwamnatin jihar ta tabbatar dukkan matakan kula da barkewar cutar suna aiki don dakile yaduwarta a cikin kankanin lokaci,” inji Nwogwugwu.
Hukumar Yaki da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce kawo yanzu mutum 172 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin kasa a 2022, sannan cutar ta kashe mutum hudu.