✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin sojin Nijar ta sako dan kasar Faransa da ta tsare

Gwamnatin sojin Nijar ta sako wani dan kasar Faransa da ta tsare bayan da dangantaka ya kara tsami tsakanin kasashen biyu.

Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta sako wani dan kasar Faransa ta ke tsare a hannunta, bayan da dangantaka ya kara tsami tsakanin kasashen biyu.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa, ta bayyana jin dadinta a safiyar Alhamis da sakin Stephane Jullien, wanda gwamnatin sojin Nijar ta tsare shi bayan da jijiyoyin wuya suka tashi tsakanin kasashen biyu.

A ranar Talata Faransa ta yi korafi game da tsare Jullien tun ranar Juma’a da ta gabata, tana mai kira da a sako shi.

Jullien, dan kasuwar Faransa ne mazaunin Nijar kuma wakiltin ’yan kasarsa a ofishin jakadancinta da ke birnin Yamai.

Dangantakar Faransa da Nijar ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yuli, wanda babban abokin kasar Turawan ne.

Faransa na da sojoji 1,500 da ta girke a Nijar domin yakar ’yan bindiga masu ikirarin jihadi a yankin Sahel, inda ta tsaya kai da fata wajen taimakon gwamnatin Bazoum ta wannan fuska.

Ta ayyana gwamnatin sojin Nijar a matsayin haramtacciya, ita kuma gwamnatin sojin ke neman sojojin turawan su kwashe kayansu daga kasar.

A makon jiya dai, rundunar sojin Faransa ta ce ta fara tattaunawa da sojojin Nijar kan batun janye sojojin Faransa daga kasar.