Gwamnatin mulkin soji a Jamhuriyyar Nijar karkashin Janar Abdourahamane Tchiani ta sanar da yanke alaƙar soji da Amurka.
Mai magana da yawun gwamnatin, Kanar Abdourhamane Amadou ne ya yi shelar hakan a kafar talabijin mallakin gwamnati a cikin daren jiya na Asabar.
Sanarwar ta ce Jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata alaƙar ayyukan soji da Amurka sakamakon rashin gamsuwa da halaccin yarjejeniyar da aka fake da ita don shigo da dakarun sojin Amurka a kasar ta Nijar a 2012 cikin wani yanayi mai kama da tilastawa ba don rai ya so ba.
- ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga, sun kwato makamai a Kaduna
- Mahara sun sace shugaban jam’iyyar PDP a Edo
Wannan dai na zuwa ne sakamakon gamsuwa da rashin samun wata gudunmawar da ta dace daga Amurka a yunkurin murkushe matsalolin tsaron da ke sanadin rasa rayukan sojoji da al’ummar Nijar.
Da wannan ne kuma gwamnatin ta Nijar ta umurci dakaru 1100 da Amurkar ta girke a sansanoni daban-daban su fice daga kasar ba tare da bata lokaci ba a cewar wannan sanarwa.
Wannan sabon al’amari na zuwa ne a washegarin rangadin da wata tawagar jami’an gwamantin Amurka ta gudanar a Nijar a karkashin jagorancin mataimakiyar sakataren gwamnatin Amurka mai kula da harkokin Afirka, Molly Phee.
A yayin rangadin ne tawagar Molly Phee ta tattauna da Firaiminista Ali Lamine Zeine da wasu mukarraban gwamnatinsa dangane da shirin mayar da Nijar tafarkin dimokuradiya.
Sai dai bayanai sun ce yunkurin ganawar Amurkawan da Janar Abdourahamane Tchiani ya ci tura, lamarin da ke fayyace alamun an yi watsewar baram baram a zaman da ya hada jami’an kasashen biyu.
A wani bangare na sanarwar da Kanar Abdourhamane Amadou ya fitar, hukumomin na Nijar sun nuna rashin gamsuwa da abin da suka kira muguwar halayyar da sakatariya Molly Phee ta nuna a yayin ziyarar ta ranakun Talata, Laraba da Alhamis din da suka gabata .
Hukumomin na Nijar sun yi zargin cewa tawagar ta Amurka ta saba ka’ida ta hanyar zuwa ba tare da wata sanarwa ta gargadi ba.
Hulda a tsakanin Nijar da kasashen Rasha da Iran na daga cikin batutuwan da sanarwar ta hukumomin mulkin sojan Nijar ta tabo, suna masu kare matsayin kasar da suka ce tana da ‘yancin zabin kawayen da suka dace da manufofinta a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta.
Tun bayan da sojojin suka yi juyin mulki ne a ranar 26 ga watan Yuli na shekarar da ta gabata suke daukar irin wannan mataki na yanke hulda da kasashen yamma, tare da kulla dangantakar tsaro da Rasha.
Amurka da Nijar suna da yarjejeniyar soji tun 2012, wadda a karkashinta dakarun Amurka da ke hamada suke amfani da kananan jiragen sama marassa matuka wajen yakar kungiyoyi masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.
Amurka wacce ta yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi, ta dakatar da bai wa Nijar tallafin da ta saba bayarwa a fannoni da dama cikin har da fannin tsaro.
Haka kuma, ta sha yin hannunka mai sanda kan dukkan wani yunkurin kulla mu’amula da kasashe irinsu Rasha masu amfani da sojan haya a matsayin hanyar kula da sha’anin tsaro.
Juyin mulkin na Nijar ya kasance daya daga cikin guda takwas da sojoji suka yi a yankin Afirka ta yamma da kuma Afirka ta tsakiya.
Sauran ƙasashen da sojoji suka yi juyin mulkin bayan Nijar su ne Burkina Faso, da Mali, da Guinea da kuma Chadi, kodayake ita Chadi ɗan marigayi shugaban ƙasar ne ya karɓe iko bayan kashe mahaifinsa Idriss debby a fagen yaƙi da ‘yan tawaye.
Juyin mulkin ya sa kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS sanya wa Nijar takunkumin tattalin arziki.
Bayan wani lokaci kuma kasashen Nijar, da Mali, da Burkina Faso, suka bayyana ficewa daga kungiyar ta Yammacin Afirka.
Sai dai kuma a baya-bayan nan ne kungiyar kasashen ta janye dukkanin takunkumin da ta sanya wa Nijar din tare da bayar da umarni da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya yi na bude iyakokin kasarsa da Nijar din.