✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Nijeriya ta yi sakaci kan kisan Sarkin Gobir — Atiku

Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama’a.

Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin ƙasar da sakaci kan kisan da aka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

A wannan Larabar ce aka samu labarin mutuwar sarkin wanda ’yan bindigar da ke garkuwa da shi suka kashe, bayan kasa kai musu kuɗin fansar da suka buƙata domin sakin sarkin tare da ɗansa.

Shuaibu Gwanda Gobir, wanda shi ne Magaji Garin Gobir kuma ɗaya daga cikin masu naɗin sarki, ya ce labari ya ishe su cewa masu garkuwar sun kashe sarkin ne a ranar Talata.

Sai dai cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, jagoran adawa a ƙasar, ya ce sakacin gwamnati da na jami’an tsaro ne suka janyo mutuwar sarkin.

“Nuna halin ko’in kula da gwamnati ta yi, da rashin ingantaccen tsari daga jami’an tsaro sun taimaka wajen yaɗuwar irin waɗannan abubuwa masu sanya raɗaɗi a zuciya a lokutan baya-bayan nan,” in ji Atiku.

“Yana da muhimmanci mu ƙara jaddada wa gwamnati cewa dole ne ta samar da tsaron rayukan jama’a ta yadda mutane ba za su rayu cikin fargabar fuskantar irin haka ba.”

Atiku Abubakar ya nuna alhininsa kan rasuwar sarkin tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai da ɗaukacin al’ummar masarautar Gobir, da Gwamnatin Sakkwato kan mutuwar sarkin da ya bayyana a matsayin mai “cike da tashin hankali.”

A cikin wannan makon ne dai aka ga sarkin a wani bidiyo yana neman Gwamnatin Sakkwato ta biya ’yan bindigar kuɗin fansar da suka buƙata, inda ya ce idan wa’adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.

Makonni uku da suka gabata ne ’yan bindigar suka yi garkuwa da sarkin a yankin Kwanar Maharba, lokacin da yake kan hanyar komawa gida bayan halartar wani taro a cikin garin Sakkwato.