✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Mali ta dakile yunkurin juyin mulki

An murkushe yunkurin saboda kwarewar hukumomin tsaro.

Gwamnatin Mali ta sanar da dakile yunkurin wani juyin mulki da aka so yi mata a makon jiya.

Hukumomi a Malin sun sanar da karfafa matakan tsaro a iyakokin kasar bayan wannan yunkuri.

A wata sanarwar da ta fitar, fadar mulki ta Bamako ta ce ta kama sojin da suka kudiri aniyar mayar da hannun agogo baya.

Sanarwar ta ce an yi yunkurin ne a daren 11 zuwa 12 ga wannan watan, tare da zargin kasashen yamma da hannu kai tsaye wajen kitsa makarkashiyar, sai dai kuma gwamnatin ba ta yi wani karin haske kan kasashen da take zargi ba.

A jawabin da aka bayyana a kafar talabijin, “wasu tsiraru jami’an sojin Mali sun yi yunkurin kai hari a ranar 11 a 12 ga watan Mayun 2022.”

“Wadannan sojoji sun samu goyon bayan kasashen yammaci. An murkushe yunkurin saboda kwarewar hukumomin tsaro.”

Sanarwar ta kara da cewa wadanda aka kama za a gurfanar da su, amma ba tare bayyana sunayensu ba.

Wasu majiyoyi sun ce kusan mutum 10 aka kama ake tsare da su.

Tuni dai mahukuntan na birnin Bamako suka kara tsaurara matakan tsaro kan iyakokin fita daga babban birnin da ma daukacin iyakokin kasar baki daya.

Tun bayan juyin mulkin da soji suka yi wa wata gwamnatin farar hula ta rikon kwarya a watan Mayun bara, sabbin mahukuntan na Mali suka fada zaman doya da manja da wasu kasashen duniya ciki har da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, lamarin da ya kai ga Faransar janye sojojinta da ke yaki da ta’addanci.